1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Najeriya sun tsere wa sansaninsu

Salissou Isssa/Lateefa Mustapha Ja'afarJanuary 6, 2015

Bababan hafsan sojojin Najeriya Air Chief Marshal Alex Badeh ya amince cewar 'yan Boko Haram sun kwace ikon sansanin sojojin kasa da kasa da ke Baga na jihar Borno.

https://p.dw.com/p/1EFmQ
Hoto: picture-alliance/AP

Sansanin wanda ke a kan iyakar Najeriya da kasar Chadi ya shiga hannun 'yan kungiyar ta Boko Haram ne a karshen mako. Badeh ya shaida wa manema labarai cewa dakarun Najeriya ne kadai a sansanin sojojin yayin da 'yan ta'addan na Boko Haram suka kai farmaki. Ya kara da cewa tuni kasashen Chadi da Nijar suka janye sojojinsu daga wannan sansani, sai dai bai yi karin bayani dangane da dalilin janye dakarun kasashen biyu ba.

Air Chef marshar Badeh ya musanta cewa kasashen da ke makwabtaka da Najeriyar sun fita daga rundunar hadin gwiwar da ta hadar da dakarun kasar Kamaru. Shaidun gani da ido sun bayyana cewa sojojin Najeriyar sun tsere ne bayan da makamansu suka kare a yayin da suke fafatawa da 'yan Boko Haram. Ko da aka tambayeshi kan wannan batu, Badeh ya ce "me yasa ba za su gudu ba?" sai dai bai yi karin haske ba.