1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin gwamnatin hadin kan kasa sun hallaka a Libiya

Salissou Boukari
May 27, 2017

Rundunar sojojin da ke biyayya ga gwamnatin hadin kan kasa a Libiya, ta sanar mutuwar dakarunta 52 sakamakon wani fada da suka gwabza a wata unguwa ta manyan mutane da ke birnin Tripoli.

https://p.dw.com/p/2dgCk
Libyen Konflikt - Soldaten
Sojojin Gwamnatin LibiyaHoto: Getty Images/AFP/M. Turkia

Sai dai duk da haka sun kori wadanda suka kawo musu harin da ke bukatar kwace wasu yankuna na birnin Tripoli da ake zaton mayakan Fajir Libiya ne. A wannan rana ta farko ta Azumin watan Ramadan, kura ta lafa a birnin na Tripoli, ko da yake an yi ta jin karar harbe-harbe a yankin kudancin birnin. Tuni dai Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da hauhawar tashin hankali a birnin na Tripoli, inda ya yi kira ga bangarorin biyu da su dakatar da fadan.

Sojojin da ke biyayya ga gwamnatin hadin kan kasar ta Libiya, sun sanar ta shafin su na Facebook cewa sun kwace gidan kason da ake tsare da manyan jami'an gwamnatin marigayi Muammar Ghaddafi, cikin su kuwa har da Firaministansa na karshe Baghdadi Al-Mahmoudi, da kuma tsohon shugaban hukumar leken asirin kasar Abdallah Senoussi.