1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Iraki sun kwace iko da Kirkuk

Abdul-raheem Hassan
October 16, 2017

Dakarun gwamnatin Bagadaza, sun samu nasarar karbe iko da cibiyoyi mafi mahimmanci da suka hada da sansanin sojoji mafi girma da filin jirgi da yankunan albarakatun mai da sojojin Kurdawa ke iko da su.

https://p.dw.com/p/2lw9J
Irak Kurden-Peschmerga in Snuny bei Sinjar
Hoto: picture-alliance/AP Photo/B. Janssen

Wannan somame dai na zuwa ne makonni kalilan bayan da Kurdawan suka gudanar da zaben raba gardama da ke neman raba gari da gwamnatin Bagadaza, matakinda ya jawo kasashe makota katse dangatakar kasuwanci da su.

A yanzu dai sojojin gwamnatin Iraki sun yi nasarar sauke tutar mayakan Kurdawa da ke shawagi a gine-ginen gwamnati a birnin Kirkuk, birni mafi mahimmanci mai dauke da rijiyoyin mai da ke jawo takkadama tsakanin gwanatin Iraki da 'yan awaren Kurdawan.

To sai dai yayinda wasu ke cike da murnar maido da yankin karkashin ikon sojojin gwamnati, wasu mazauna garuruwan da ke kewaye da birnin na Kirkuk, na ci gaba da fice daga yankin a wani mataki na gudun hare-haren daukar fansa da ka iya ritsawa da iyalansu, kamar yadda Yousef Ismail wani magidanci ke cewa:

"Mun nufi birnin Irlib saboda yanayin na ci gaba da daukar zafi, sojoji daga dukkannin bangarori sun yi mana kawanya, babu damar ci gaba da rayuwa a Kirkiuk."