1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Mali sun kutsa inda ake garkuwa da mutane

Suleiman BabayoNovember 20, 2015

Sojoji na musamman sun kutsa cikin otel da ake garkuwa da mutane170 da ke birnin Bamako fadar gwamnatin kasar Mali.

https://p.dw.com/p/1H9S5
Mali Geiselnahme Hotel in Bamako
Hoto: H. Kouyate/AFP/Getty Images

Dakarun musamman na kasar Mali sun kutsa cikin otel da ake garkuwa da kimanin mutane 170. Shaidun gani da ido da 'yan sanda suka tabbatar. Rahotanni sun nuna cewa an hallaka mutane uku daga cikin wadanda ake garkuwa da su.

Tsageru masu kaifin kishin addinin Islama kimanin 10 dauke da makamai suka yi garkuwa da wannan da ke birnin Bamako fadar gwamnatin kasar. Majiyoyin tsaro sun ce maharan sun shiga cikin wannan otel da motar da take dauke da lambar jami'an diplomasiya. Majiyoyin Faransa sun tabbatar da cewa akwai 'yan kasar a cikin wannan otel haka kasar China ta ce akwai 'yan kasarta bakwai, yayin da Turkiya ta ce akwai ma'aikatar kamfanin sufurin jiragen saman kasar shida.

Shugaba Ibrahim Boubakar Keita na kasar ta Mali ya katse ziyarar da yake yi a kasar Chadi domin komawa gida bayan garkuwa da mutanen.