1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dauki sojojin Siriya ga Kurdawa

Gazali Abdou Tasawa MAB
October 14, 2019

Dakarun sojan Siriya na ci gaba da dannawa a wanann Litinin zuwa iyakar kasarsu da Turkiyya domin kawo dauki ga mayakan Kurdawa a fadan da suke da sojojin Turkiyya.

https://p.dw.com/p/3RFzX
Syrien Tal Tamr Syrische Armee trifft in Kurdengebieten ein
Hoto: AFP via Getty Images

Dakarun sojan kasar Siriya na ci gaba da dannawa zuwa iyakar kasarsu da Turkiyya kwana daya bayan da Kurdawan Siriyar suka sanar da cimma wata yarjejeniya da gwamnatin Siriyar domin taka birki ga farmakin da sojojin Turkiyyar suka kaddamar a arewacin kasar ta Siriya.

 Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP ya ruwaito sojojin na gwamnatin Bashar al-Assad sun isa birnin Tal Tamr inda suka ja daga a bakin garin wanda ke a nisan kilomita kimanin 30 da kudancin birnin Ras al-Ain inda ake ci gaba da gumurzu tsakanin mayakan Kurdawan masu samun goyon bayan mayakan 'yan tawayen Siriya da kuma sojojin Turkiyyar.

 Daga nata bangare Kungiyar OSDH da ke sa ido a rikicin kasar ta Siriya ta sanar da cewa sojojin Siriyar na a nisan kilomita shida ne kawai da wurin da ake gwabzan fadan. Tun dai bayan da Amirkawa suka janye sojojinsu daga yankin na Kurdawan Siriya. mayakan Kurdawan suka nemi ala dole dauki daga sojojin Bashar al-Assad domin kare su daga farmakin Turkiyyar.