Sojojin Siriya sun kwato wani yanki daga IS

Dakarun gwamnatin Siriya sun kwato wani sansanin sojin sama na kasar daga ikon mayakan kungiyar IS, a ci gaba da fafatawar da suke yi da mayakan na tarzoma a kasar.

Gamayyar kungiyoyi da ke kare hakki jama'a a kasar Siriya ta ce mayakan da suka yi gamon taron dangi, sun danna tare da kwato sansanin na soji da ke yankin Jirrah a arewacin birnin Aleppo.

Ana dai ci gaba da gumurzu tsakanin bangarorin biyu, kamar yadda kungiyar ta tabbatar kuma ba a kai ga samun cikakkun alkaluman wadanda suka mutu a artabun na wannan Asabar.

Shaidu sun ce dakarun na ci gaba da kutsawa garin Maskanah da ake ganin babbar tunga ce ta mayakan na tarzoma a kewayen na Aleppo, inda ake ta ganin rubuce-rubucen da ke dauke da alamun kungiyar ta IS.


Bayanai masu kama

Rahotanni masu dangantaka