1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Sudan sun kai hare-hare a Sudan ta Kudu

Abdourahamane HassaneNovember 14, 2014

An ba da rahoton cewar jiragen sama na yaƙi na Sudan, sun yi ruwan bama-bamai a Sudan ta Kudu a wani yankin da ke kan iyaka da birnin Khartoum.

https://p.dw.com/p/1Dn7l
Konflikt im Südsudan Regierungssoldaten 25.12.2013
Hoto: Samir Bol/AFP/Getty Images

Da yake magana da wani gidan rediyio mai zaman kansa kakakin rundunar sojojin Sudan ta kudu Philip Aguer. Ya ce sojojin na ƙasar Sudan sun jefa bama-baman ta jiragen sama a garin Maban da ke a yankin Nilu,inda 'yan gudun hijira kusan dubu 125 suka gujewa yaƙin da ake yi a gabashin Sudan.

To sai dai ɓangaran gwamnatin ta Sudan ya musanta zargin cewar ya kai hare-haren a makofciyar ƙasar.Wannan zargi na zuwa ne a dai dai lokacin da gwamnatin Sudan,take yin wata tattaunawa ta neman sulhu tsakaninta da 'yan tawayen yankin Nilu a ƙasar Habasha.