1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Somalia na neman tallafi na dalar Amurka miliyan 60

December 29, 2005
https://p.dw.com/p/BvEe

Shugaban kasar Somalia na wucin gadi, wato Yusuf Abdulla ya daukaka kira ga kasashen duniya na neman tallafin Dalar Amurka miliyan 60, don agazawa miliyoyin yan kasar dake fama da fari da kuma karancin ruwan sha.

Shugaban na Somalia yaci gaba da cewa, akwai bukatar agajin gaggawa a fadin kasar ta Somali baki daya, musanmamma bisa la´akari da irin halin da miliyoyin yan kasar ke ciki.

Abdullah Yusuh har ila yau ya tabbatar da cewa , matukar ba a kawowa al´ummar kasar agajin gaggawa ba, to babu shakka wasu miliyoyin yan kasar ka iya fadawa cikin matsalar ta rashin abinci da kuma karancin ruwan shan.

A waje daya kuma, wata sanartwa data fito daga kasar Kenya ta nunar da cewa kasar ta Somalia na bukatar tallafi ne na kudi da abinci da kyakkyawan ruwan sha da magunguna da kuma sauran abubuwan more rayuwa na yau da kullum.