1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sosoji a Masar sun amince da takarar Al-Sissi

January 27, 2014

Sojojin kasar Masar sun bada amincewarsu ga takarar Janar Abdel Fattah al-Sissi, a matsayin dan takara a zaben shugaban kasar da za a yi nan gaba a kasar.

https://p.dw.com/p/1Ay5C
Ägypten Verteidigungsminister Abdel Fattah al-Sissi Fernsehbild
Hoto: AFP/Getty Images

Sai dai wannan labari na takarar Al-Sissi wanda bai dade da kasancewa a matsayin Marshal ba, bai bada wani mamaki ba.

Abun da ake jira a halin yanzu shi ne sanarwar murabus ko shiga ritayar sabon Marshal din daga matsayinsa na soja, kasancewar kundin tsarin mulkin kasar ya haramta wa duk wani soja zama dan takarar shugabancin kasa a Masar.

Tuni dai tun a ranar Lahadin nan Adly Mansour, wanda Janar Sissi ya nada a matsayin shugaban rikon kwarya lokacin da aka kifar da gwamnatin Mohammed Morsi, ya sanar da cewa za a yi zaben shugaban kasar kafin na 'yan majalisar dokoki nan da watanni uku masu zuwa.

Inda ake ganin cewa wannan wani tsari ne kawai da zai bai wa Al-Sissi damar lashe zaben, sannan ya samu rinjaye a majalisar kasar da za a zaba bayan ya zama zababben shugaban kasa.

Sabili da haka ne a wannan Litinin din shugaba Mansour ya nada Janar Sissi a matsayin Marshal wanda ya fi ko wane sojan kasar ta Masar girma.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Mohammad Nasiru Awal