1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Steinmeier a Izraela

November 1, 2007

Ziyarar ministocin jAmus biyu a yankin gabas ta tsakiya

https://p.dw.com/p/C14m
Frank Walter Steimeier
Frank Walter SteimeierHoto: DW/F.Craesmeyer

Ministan harkokin waje na tarayyar jamus Frank Walter Steinmeier dake rangadin aiki a yankin gabas ta tsakiya,ya bayyana yiwuwar kakabawa Iran takunkumi,a bangaren kungiyara tarayyar turai EU.

Frank Walter Steinmeier,yayi wannan furucin ne bayan goyon bayan jamus da Izraela tayi dangane da barazanar kera makaman nuclear da tace,abokiyar gabar ta Iran keyi.Ya fadawa taron manema labaru a birnin Tel Aviv cewar,jamus bata da raayi daya sha banban dana Amurka da sauran kasashen turai,idan har Iran bata bada bayanan da ake bukata ba,adangane da shirin nuclear da ake zarginta da aiwatarwa.

Steinmeier yace iran nada lokaci har zuwa tsakiyann wata mai kamawa ,na tabbatarwa da kasashen yammaci na turai cewar shirin nuclearn tza nada kyawawan manufa,amma ba sarrafa makaman Azom ba.

Jamus dai na daya daga cikin mayanyan kasashe shida,masu fada aji a duniya wadanda kuma ke tattauna batun Nuclearn kasat ta Iran,wadda Izraela da sauran kasashebn turai ke zargin makaman atom ne,batu da ita kuma Iran ta karyata.

Prime ministan Izraela Ehud Olmert ya jadadda muhimmancin da manufofin jamus,adangane da kara kakabawa Iran takunkumi.

A wani lokaci nan gaba kadan cikin wannan shekara nedai,ake saran komitin sulhu na mdd ,zai kakabawa Iran din karin takunkumi,bayan hukumar kula da harkokin nuclear ta Mdd ta gabatar da rahotan sakamakon hadin kan da Iran din take bawa masu binciken makamai.

Adangane da shirye shiryen taron sulhu da Amurka zata dauki nauyin gudanarwa tsakani Izraela da Palasdinu kuwa,Olmert ya fadawa ministan harkokin wajen jamus dake ziyara cewar ,bangarorin biyu sun gana.

Dayake tofa albarkacin bakinsa dangane da wannan taron kuwa,Steinmeier yace turai na muradin bada dukkan tallafi na kudi wa yankin palasdinawa,idan har bangarorin biyu sun amince da bukatar hakan.

Bugu da kari a yau ne kuma ministan tsaron Izraelan Ehud Barakya gana da takwaransa na jamus Franz Joseph Jung a birnin Tae Aviv,inda suka tabo batutuwan dangantakar tsaro da diplomasiyya.