1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta jaddada goyon baya ga Ukraine

Suleiman Babayo LMJ
October 26, 2022

Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya kai ziyarar aiki zuwa Ukraine, inda ya jaddada goyon bayan Jamus ga Kiev a daidai lokacin da Rasha ke ci gaba da mamaya a kasar.

https://p.dw.com/p/4IijM
Ukraine Kiev | Shugaban Kasar Jamus | Frank-Walter Steinmeier | Volodymyr Zelenskiy
Shugaban kasar Jamus Steinmeier da takwaransa na Ukraine ZelenskiyHoto: GLEB GARANICH/REUTERS

Wannan ziyarar ta Shugaba kasar ta Jamus Frank-Walter Steinmeier dai, na zuwa watanni shida bayan sukar da ya fuskanta kan tsawon lokaci da ya kwashe yana goyon bayan manufofin mahukuntan Rasha. Yayin ziyarar shugaban kasar Jamus din ya gana da manyan jami'an gwamnatin Ukraine, a wani gari da ke Arewa maso gabashin birnin Kiev fadar gwamnatin kasar. Suna tsaka da ganawar an saki sautin gargadi na yiwuwar kai hare-hare daga dakarun Rasha, lamarin da ya tilasta musu neman mafaka a wuraren da aka tanada. Ga abin da Steinmeier ke cewa: "Yanzu haka ana fuskantar hare-haren makamai masu linzami na Rasha da jirage masu sarrafa kansu da suke lalata gine-gine a cikin kasar, yana da tasiri gare ni da na zo nan tare da mutanen Ukraine."

Jamus | Ziyara | Ukraine | Shugaban Kasa | Frank-Walter Steinmeier
Steinmeier da tawagarsa, sun nemi mafaka bayan bayar da sanawar hari a UkraineHoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Steinmeier ya kuma bayyana wasu daga cikin taimakon da Jamus ta samar ga kasar ta Ukraine da ya hadar da bayar da kayayyakin amfani lokacin hunturu, kama daga injinan samar da wutar lantarki da fasahar dumama wuri cikin dazuzzuka da kayayyakin gyara na tafi da gidanka da na dumama ruwa. Kasashen Yammacin Duniya na ci gaba da karfafa matakan taimakon Ukraine, domin kare kanta daga hare-haren na dakarun Rasha. Kuma gwamnatin Ukraine ta jinjina, musamman yadda Jamus ta tashi tsaye domin taimakon kasar. Shugaba Volodymyr Zelensky na kasar ta Ukraine ya yaba da matakin taimakon kasarsa da Jamus ke yi, musamman kan gina kasar bayan yaki. Wannan ke zama ziyarar Steinmeier ta farko a kasar ta Ukraine, tun bayan kutsen da Rasha ta kaddamar a ranar 24 ga watan Fabarairun wannan shekara ta 2022 da muke ciki.