1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: Fafutukar neman samun canjin mulki

Mwaura, Wanjiku ZAK
January 31, 2019

Jama'a da dama na ci gaba da gudanar da znga-zanga akan titunan kasar Sudan tare da kiraye-kirayen shugaban kasar Omar al-Bashir ya gaggauta sauka daga mukaminsa.

https://p.dw.com/p/3CV4S
Sudan Khartum Kundgebung Anhänger von Präsident Al-Baschir
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Hjaj

Zanga-zangar dai ta samo asali ne sakamakon karin kudin biredi tun a watan da ya gabata kafin daga baya ta juye ta zama ta neman shugaban kasar Omar al Bashir da ya sauka daga mukaminsa. Yanzu haka dai mako na takwas ke'nan da al'ummar kasar daga garuruwa daban-daban ke neman sauyin gwamnati a Sudan, a bangaren kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun baiyana cewar adadin  mutanen da suka rasa ransu ya kai 100 yayin da gwamnati ta baiyana mutane 29 da suka mutu. Jam'iyyun siyasa sun raba gari da gwamnati, jam'iyya ta baya-bayan da ta sanar da yin hannu riga da gwamnatin kasar ta sudan itace jam'iyyar Umma.