1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al-Bashir zai bakunci kotun ICC

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 11, 2021

Gwamnatin kasar Sudan ta bayyana aniyarta na mika tsohon shugaban kasar Omar Hassan al-Bashir ga kotun kasa da kasa da ke hukunta masu aikata laifukan yaki wato ICC da ke birnin The Heague na kasar Netherlands.

https://p.dw.com/p/3yrSm
Gipfeltreffen der Arabischen Liga in Doha Omar Hassan Al Bashir
Omar Hassan al-Bashir ya kawashe shekaru yana mulki kafin kifar da gwamnatinsaHoto: picture-alliance/abaca/A. A. Rabbo

Ministar harkokin kasashen waje ta kasar Sudan din Mariam al-Mahdi ce ta sanar da hakan ga kamfanin dillancin labaran kasar Suna, inda ta ce za su mika al-Bashir da aka kifar da gwamnatinsa a shekara ta 2019 da sauran wadanda kotun ta ICC ke nema zuwa birnin na The Heague. Da ma dai tun a shekara ta 2008 ne kotun ta ICC ta nemi a mika mata al-Bashir din, bisa zarginsa da aikata laifukan yaki a yankin Dafur na kasar ta Sudan.