1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Suka bisa kudin raya kasa

Usman ShehuDecember 24, 2013

Al'ummomin arewa maso gabashin Najeriya sun soki kason raya yankin da gwamnatin Goodluck Jonathan ta bayar musamman a jihohin ake dokar ta-baci

https://p.dw.com/p/1AgWa
Murtala Nyako
Murtala Nyako, gwamnan jihar AdamawaHoto: DW/U. Shehu

Sun dai kira sunan taimako, sun kuma ce suna shirin raya kasa, to sai dai kuma sun kare da harzuka al'ummar yankin arewa maso gabashin Tarayyar Najeriya da suka ce da alamun rainin arziki, cikin yunkurin mahukuntan kasar na agaza musu.

Gwamnatin kasar dai ta ce ta ware tsabar kudi har Naira milliyan dubu biyu da nufin tallafawa al'ummar da suka dauki tsawon lokaci suna fuskantar matsalar boma bomai ta yan Boko Haram. Kudin kuma da fadar gwamnatin kasar ta Abuja ta ce za su tafi wajen sake farfado da tattalin arzikin al'umma dama harkokin ilimi, da zamantakewar da matsalar ta kai ga gurguntawa.

Shugaba Goodluck Jonathan
Hoto: Pius Utomi ekpei/AFP/Getty Images

To sai dai kuma adadin da ke zaman kasa sosai da Naira miliyan dubu dari da goma sha daya, da Abujar ta ce za ta kashe ga dan uwansa na Niger-Delta dai, a fadar Sanata Ahmed Lawan da ke zaman dan majalisar dattawan kasar daga jihar Yobe da kuma ya fitar da sanarwar Allah tsine, sun yi kadan sun kuma kama hanyar raba kan sassan kasar tsakanin yan bora da yan uwansu yayan mowa.

Fadi ka mutu da suna na tallafi ko kuma kokari na rage radadin rikicin na kungiyar ta Boko Haram dai, a baya shugaban kasar ya ce al'umar yankin za su kalli daban a kokari na share hawayensu, dama sake dora su bisa turba ta ci-gaba a arewa maso gabas, da ke zaman ta baya ga dangi a kusan kowace harka.

Civilian JTF
Matasa masu yaki da Boko HaramHoto: picture-alliance/AP/Abdulkareem Haruna

Ana ma dai kallon adadin a matsayin alamun da sannu a hankali ke neman gaskata, ikirarin tsohon shugaban kasar Chief Olusegun Obasanjon, wanda ya ce mahukuntan na Abuja ba su da gaskiya ga kokarin shawo kan matsalar da ke barazana ga daukacin kasar ta Najeriya yanzu haka. Ko bayan miliyan dubu dari da goma sha dayan ta badi dai, a baya mahukuntan kasar sun kai ga kisan dubun miliyoyi a cikin yankin Niger-Delta da ya fuskanci fafutuka shigen irin wannan, amma kuma aka kai ga ragin tasirin ta sakamakon horar da dubban matasan da suka dauki makamai suka gurgunta daukacin harkokin man kasar ta Najeriya.

Kashim Shettima, Gouverneur von Borno State, Nigeria
Kashim Shettima, gwamnan jihar BornoHoto: DW

Abun da kuma a cewar Garba Umar Kari da ke zaman wani masani na harkokin siyasa da zamantakewa, ke nuna alamu na rashin ya dace dama rashin ko in kula ga halin da daukacin al'ummar yankin na arewa maso gabas ke ciki a yanzu.

Daukacin jihohi ukun da ke cikin tsarin dokar ta-bacin kasar ta Najeriya dai, na zaman jihohi na adawar da daga dukkan alamu ba sa cikin zuciyar masu juya al'amuran kasar ta Najeriya a Abuja, abun kuma da ke nufin samun hankali kadan cikin kokarin tallafi ga yakin da ke cikin shekarar sa ta hudu da kuma ya kai ga asara ta dubban miliyoyi na kudi.

Mawallafi: Ubale Musa

Edita: Usman Shehu Usman