1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sumame kan masu bore a Hong Kong

Ahmed SalisuOctober 17, 2014

Jami'an tsaro a Hong Kong sun yi dirar mikiya kan masu rajin girka dimokradiya inda suka cire shingaye da tantunan da suka girka don toshe wasu manyan hanyoyi a birnin.

https://p.dw.com/p/1DWqi
Proteste in Hongkong 17.10.2014
Hoto: Reuters/Carlos Barria

Wannan sumamen da jami'an tsaron suka yi a lardin Mong Kok dai shi ne irinsa na uku a 'yan kwanakin da suka gabata a yunkurinsu na ganin masu zanga-zanga sun bar kan titunan da suka mamaye a birnin.

Hakan dai na zuwa ne bayan da shugaban yankin Leung Chun-ying ya nemi kashe rutar rikicin da yanki ke fuskanta ta hanyar farfado da tattuanawar da ta rushe a baya tsakanin gwamnatinsa da masu rajin tabbatar da dimokradiyya wanda galibinsu dalibai ne.