Taba Ka Lashe: 22.11.2017

Wasu mawaka a Nijar sun shirya sabbin wakokin wayar da kai ga al'umma da nufin cusa masu kaunar kasa da son juna.

A jamhuriyar Nijar wasu mawaka sun shirya sabbin wakokin wayar da kai ga al'umma da nufin cusa masu kaunar kasa da son juna, a wani yunkuri na canza masu dabi'a domin ma'ala ta inganta. Suna amfani da wakokin a wuraren taron jama'a da ma ta kafafen yada labaru da kuma hanyoyin sadarwa na zamani don tunzara al'umma ga amfana da sakonsu na nuna kishin kasa. 
 

Bayanai masu kama