1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taba Ka Lashe: 28.02.2018

Salissou Boukari
March 2, 2018

A duk shekara ne dai ake gudanar da bikin gwadin al'adun galgagiya na Abzinawa da ake kira Festival de l'Air, inda tsawon kwanaki uku jama'a daga ko'ina ke halartar wannan biki a jihar Agadez a arewacin Jamhuriyar Nijar.

https://p.dw.com/p/2tbi1
Bildergalerie afrikanische Kopftuchmode
Hoto: DW/T. Amadou

Shi dai tsarin farko da aka yi na wannan bikin gwada al'adun na Abzinawa an tsara shi ne ta yadda za a rinka yin shi na karba-karba tsakanin kananan hukumomin yankin na AIR, sai dai kuma wajen aiwatarwa ana iya cewa garin na Iferouan inda a nan ne aka soma wasa na farko shekaru 17 da suka gabata, ya kasance kuma nan ne ake gudanar da akasarin wasannin na "Festival de L'Air" domin kuwa wannan shi ne karo na 10 da ake yi a garin na Iferouan.