1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taba Ka Lashe: 28.06.2017

Mohammad Nasiru Awal
June 30, 2017

Tashin gwauron zabi da kudin hayar gida ya yi a kasar Spaniya na janyo matsaloli ga 'yan haya masu karamin karafi.

https://p.dw.com/p/2fhSF

Kungiyoyin 'yan hayan gida a kasar Spaniya sun nuna rashin jin dadinsu da wani abinda suka kira rikicin haya da ke tilasta 'yan haya barin gidajensu. Kungiyoyin na fatan kai kukansu ga gwamnatin kasar don ankarar da ita cewa samun gidan haya a manyan biranen kasar irinsu Barcelona da Madrid na kara yin wahala, musamman ga karamin karfi, saboda tashin gwauron zabi da kudin hayan ke yi.