1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tabbatar da adalci tsakanin Al'umma

February 20, 2013

Sassa na Duniya na ci gaba da fuskantar karancin adalci a zamantakewa, batu da ya jagoranci MDD da ƙungiyoyi mikewa tsaye domin shawo kan matsalar.

https://p.dw.com/p/17i12
Hoto: BANARAS KHAN/AFP/Getty Images

Tabbatar da adalci da daidaito a tsakanin jama'a na taka muhimmiyar rawa wajen cigaban kowace al'umma. Hakan bazai kasa nasaba da ganin yadda dukkann jam'iyyun tarayyar Jamus ke muradin mayar da hankali kan wannan batu, da ake ganin zai taka rawa a yaƙin neman zaɓen ƙasa baki ɗaya.

Wani binciken da aka gudanar tsakanin kashi 71 daga cikin 100 na jamus na nuni da cewar, akwai babban giɓi dangane da wanzuwar adalci tsakanin jama'a kuma akwai yiwuwar karuwar wannan giɓi.

Ba kamar a sauran ƙasashen Duniya ba, anan tarayyar jamus a akwai wannan batu na tabbatar da adalci tsakanin jama'a, amma ba a fannin kayayyakin more rayuwa ba. Akan karawa wa kamfanonin da suka fi samun riba haraji, ayayinda harajin da mutane ke biya yana dogaro ne da abun da suke karɓa a matsayin albashinsu. Sai dai anyi amanar cewar akwai giɓi a tsarin da ake bi, tsakanin matakai daban daban, acewar Hubertus Pellengahr dake zama babban direktan sabon shirin tabbatar da adalcia fannin kasuwanci.

Dossier Afrika kochen Gericht Spezialität Essen Simbabwe
Hoto: AFP/Getty Images

Ya ce " Ga Jamusawa za'a samu tabbataccen adalci ne kaɗai idan yara suna samun dama iri guda na samun ilimi. Hakan na nufin kashi 90 daga cikin 100 na yaran. Wannan ɓangaren ma na bukatar ɗaukarmataki tarayyar Jamus".

A zahirance dai mutane na muradin ganin cewar an cimma wannan daidaito na tabbatar da adalci a fannin rayuwa ba tare da bayyanar wani banbanci ba, kuma wannan shine babban kalubale dake gaban jam'iyyu a yaƙin neman zaɓen ƙasa baki ɗaya da ke gabatowa.

Sai dai a cewar Stefan Liebig, dake zama farfesar ilimin zamantakewa a jami'ar Bielefeld, ko wace jam'iyya nada nata fassara. A yayin da masu ra'ayin gurguzu ke muradin ganin an sake tsarin kudaden shiga da arzikin ƙasa, sauran jam'iyyun sun mayar da hankali wajen ganin cewar ana samun adalci a kowane fanni na rayuwa.

Ya ce " Domin tabbatar da adalci ya zamanto wajibi ayi wa mutane kyakkyawar sakayya bisa irin ayyuka da suka gudanar. Wannan sakayya na ɓangaren tabbatar da adalci da daidaito a fannin rayuwa".

An hakikance cewar kashi 81 daga 100 a binciken da aka gudanar kan adalci a fannin rayuwa tsakanin al'umma anan tarayyar, ra'ayi ya banbanta dangane da yadda ake saka wa waɗanda ke aiki tukuru. Sun bada misalin kwararru dake ɗaukar lokaci wajen yin horo kamar harkokin wasannin motsa jiki, da kuma irin mutanen da suke aiki a mashaya.

Familie Fahrrad Sport Natur
Hoto: Fotolia/Kzenon

A nan tarayyar Jamus dai ana daɗa dasa ayar tambaya akan wannan kalma ta adalci. Wanda kuma ke kasancewar kalubale ne ga 'yan siyasa da jam'iyyun siyasa na inganta adalci a rayuwar Yara da Iyalai. A cewar Masanin ilimin zamantakewa Hubertus Pellengahr dai, cigaban tattalin arzikin ko wace kasa ya ta'allaka ne akan akan samun daman ilimi tsakanin al'ummarta.

Ya ce " Mafita itace, karfafa matasan da basu da dama ko sukuni karfin gwiwa, ta yadda za'a samu amincewa da cuɗanya dasu tun suna yara ƙanana, domin akwai riba a ilimantar da yara tun suna ƙanana".

Ra'ayi dai ya zo guda tsakanin masana da ƙwararru dangane da bukatar mikewa tsaye wajen tabbatar da adalci a zahirance tsakanin jama'a, domin hakan ne zai taimaka matuka gaya wajen samun ingantacciyar al'umma mai ci gaba ta fannin tattali da rayuwa.

( Akwai sautin rahotanni kan wannan batu a daga ƙasa)

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mohammad Nasir Awal

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani