1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tabbatar da kyakkyawan shugabanci da adalci a Najeriya

January 11, 2013

Dattawa da manyan 'yan siyasar Najeriya sun nunar da cewa kyakkyawan shugabanci da adalci su ne hanyar warware matsalar tsaro da kasar ke fuskanta.

https://p.dw.com/p/17IcU
Torbogen am Stadtrand der nigerianischen Hauptstadt Abuja, aufgenommen am Donnerstag (02.08.2007). Foto: Gero Breloer dpa +++(c) dpa - Report+++
Hoto: picture-alliance/dpa

A tarayyar Najeriya tabarbarewar tsaro yanzu haka dai ya zamo wani babban kalubale da ke barazana ga ci-gaban kasar da kuma al'ummarta. A kasar dai ana yawaita samun rikice rikice da kai wa juna hare hare musamman tsakanin matasa musulmai da kiristoci.

Wadannan da sauran su dai na daga cikin matsalolin da suka sanya kungiyoyin dattawa a Najeriya da tsaffin shugabanni su ma suka fara shigowa cikin dukkannin aikace aikacen da hukumomi da kungiyoyi suka dukufa suna aiwatarwa a wannan lokaci don bayar da tasu gudunmawar da zumar magance matsalolin da suka addabi kasar.

Alhaji Yusuf Maitama Sule dan masanin Kano wani babban jigo ne daga kungiyar dattawa arewacin Najeriya wato A.C.F. da ya bi sahun sauran kungiyoyin dake fafatukar tabbatar da samar da dauwamammen zaman lafiya a Najeriya ta hanyar fitowa ta kafafen watsa labarai ya na janyo hankalin shugabannin da cewa rashin adalci tare da danne wa talakawan kasa hakkokinsu, su ne dai musabbabin abubuwan da suka janyo wa Najeriyar kalubalen matsalar tsaro da tashe tashen hankula da suka jefa kasar cikin wani munmunan yanayi.

Nigeria Abuja Notstand
Gwamnati na ware kudi mai yawa ga bangaren tsaroHoto: picture-alliance/dpa

Jama'ar Najeriya da yawa sun fara komawa wurarensu na asali bugu da kari kuma wasu da ma sun fara yin gudun hijira a sabili da gazawar hukumomin kasar wajen daukar kwararan matakan da suka cancanta don magance rikicin kasar.

A yanzu haka dai duk da makudan kudaden da ake ware wa bangaren tsaro don gano bakin zaren wadannan rigingimu, a kullun ana samun karuwar ayyukan 'yan fashi da matami da kungiyoyin masu tsafe tsafe da yaduwar kananan makamai a hannun 'yan kasa.

Mr. Anthony Sani shi ne kakakin kungiyar tuntuba ta dattawan jihohin arewacin Najeriya da shi ma ke nuna takaicinsa dangane da tabarbarewar tsaro a cikin kasar, ya ce ya dai zamo wajibi ga dukkanin bangarorin jami'an tsaro da su ribanya kokarin da suke yi na kawo karshen ire-iren wadannan tashen tashen hankula.

Nigeria Bomb-Anschlag
Harin bam ya zama ruwan dare a wasu sassan NajeriyaHoto: Picture-Alliance/dpa

Hada karfi da karfe don shawo kan matsalar Najeriya

Wannan yunkuri dai na kawo zaman lafiya a Najeriya ya hada da 'yan kasar mazauna kasashen ketare irin su Alhaji Aliyu Sokoto wani ma'aikacin gidan rediyo na Muryar Amurka dake bukatar hukumomin arewacin Najeriya su tashi tsaye don tunkarar wadannan rikice rikice a yankinsu, inda a kara da cewa "mun rasa gane abubuwan dake sanya a arewacin Najeriya ne kawai aka fi samun tashe tashen hankula na kabilanci da siyasa tare da na addini.

A wani ci-gaban kuma a rana Juma'a kungiyoyin matasan jihohin arewa suka kammala taron koli na kwanaki 2 don zakulu hanyoyin hana ci-gaban fadace fadace da rashin fahimtar juna tsakanin mazauna arewacin Najeriya.

Akalla tantabaru sama da 200 aka sake sama yayin kammala taron a matsayin wani mataki na ganin an samu dorewar zaman lafiya a Najeriya baki daya.

Mawallafi: Ibrahima Yakubu
Edita: Mohammad Nasiru Awal