1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tabbatar da sahihin zabe a Yammacin Afirka

Ubale MusaDecember 15, 2014

Shugabannin kasashen ECOWAS sun yi nazarin hanyoyin tabbatar da karbabben zabe da ganin karshen matsalar tsaro da annobar cutar Ebola, a taron da suka yi a Abuja

https://p.dw.com/p/1E5D9
Westafrikas Staatschefs bei ECOWAS Summit
Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

Kama daga batun tsaro da zaman lafiya ya zuwa siyasa dama zamantakewar al'umma dai, sannu a hankali al'ummar yankin Yammacin Afirka na dada fadawa tsaka mai wuya dama barazana na tashin hankali a sassa daban daban na kasashenta 15.

Ko bayan matsalar annobar Ebolar da ta lamushe rayuka sama da 6,000 sannan babu alamar gajiyawa ya zuwa tashe-tashen hankali irin na Boko Haram, sannan kuma na baya-baya faduwar gaban yiwuwar rikici a kalla kasashe biyar da ke shirin yin zabe a badi dai tana kara baki da yin muni a cikin harkoki na rayuwar al'umar yankin sama da miliyan 250. Abun kuma da a wannan Litinin ya dauki hankalin shugabannin kasashen dama wakilain kasa da kasa da ke taro a Abuja da kuma ke neman mafitar sake dora yankin cikin turbar dai dai.

Shugaba Alassane Ouattara na Ivory Coast
Shugaba Ouattara na Ivory CoastHoto: Reuters

Sama da mutane 142,000 ne dai a fadar babban wakilin Majalisar Dinkin Duniya a cikin yankin Mohammed ibn Chambers, yanzu haka ke zaman gudun hijira sakamakon rikicin Boko Haram kadai.

" Rikicin Boko Haram na ci-gaba da jawo kisan babu gaira, mutanen da basu ji ba balle su gani na asarar rayukansu, sannan al'umma na rayuwa cikin halin ni 'yasu. Yawan yan gudun hijira a Chad da kamaru da Nijer sun kai mutum 142,000. A yayin kuma da mutanen da aka raba da gidajensu a Najeriya sun kai kusan 700,000."

To sai dai kuma ko bayan batun rashin tsaron dai, ana kuma tsoron sakamakon zabukan kasashen Najeriya da Togo da Ivory Coast da Burkina Faso da kuma Guinea a badi dai na iya rikicewa ya zuwa filin dagar rikici a cikin yankin da ke takama da 'yan mulkin mulaka'u a yanzu.

Ecowas Treffen in Abuja
Shugaba Jonathan da shugaban hukumar gudanarwa James GbehoHoto: Reuters

Abun kuma da a fadar salamatu Sulaiman da ke zaman babbar kwamishinar da ke kula da siyasa a Hukumar Gudanarwar Ecowas ya sanya maida hankali da nufin tabbatar da karbabben zabe a ko'ina.

To sai dai banda kokari na tabbatar da zaman lafiyar al'ummar yankin dai wani batun da ke daukar hankalin masu taron na zaman barazanar annoba ta Ebola da ta hallaka mutane sama da 6,000. sannan kuma bata nuna alamar kakkautawa. Tuni dai kasashen suka nada shugaba kasar Togo Faure Gnassingbe domin jagorantar sabon yakin da cutar da ko bayan taimako daga nesa, ke kuma kallon hada wata rundunar cikin gidan 'yan yankin domin tunkararta kai tsaye.