1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tahoua ta karbi bikin Jamhuriya a Nijar

December 18, 2017

An tsara saukar baki dubu shida da manyan baki daga kasashe irinsu na Najeriya da Mauritaniya da Mali da Burkina Faso da Mali.

https://p.dw.com/p/2pYxU
Niger Tende Festival in Zinder
Hoto: DW/L. Mallam Hami

A Jamhuriyar Nijar a ranar Litinin din nan ce ake bikin cikar shekaru 59 da kasar ta zamo Jamhuriya. Sai dai yau da 'yan shekaru kenan da mahukuntan kasar suka mayar da bikin ranar jamhuriyar a matsayin wata dama ta fasalta biranen kasar ta hanyar gudanar da gine gine na kawata biranen. Birnin Tahoua ne ke karbar bikin na shekarar bana wanda zai samu halartar dubban jama'a daga ciki da ma wajen kasar.

A ranar sha takwas ga watan Disamba na kowace shekara rana ce da tun bayan da Shugaba Mahamadou Issoufou ya hau karagar mulkin kasar ta Jamhuriyar Nijar ya ware ta da nufin zabin wata jiha da a duk shekara za a zaba don samar da abubuwa na raya jihar a kawatata, kamar kowace rana mai kamar ta yau a bana birnin Tahoua ne ya samu wannan moriya.

Junge Fulani Männer beim Nomadenfest Cure Salee im Niger
Hoto: DW

An tsara saukar baki dubu shida da manyan baki daga kasashe irinsu na Najeriya da Mauritaniya da Mali da Burkina Faso da Mali, an kuma samu halartar shugabanin kasa daga cikin kungiyar G5 Sahel.

Wasu 'yan Nijar da ke zaune a kasashen waje da suka kwashe shekaru da dama a kasashe kamar su Amirka sun dawo gida don ganin yadda wannan salla za ta gudana kuma a cewar Moutari Azarori garin Tahoua ya sauya sosai ganin yadda aka samar da abubuwa da gine-gine na ci gaba.

Haka dai za a ci gaba da gudanar da irin wannan salla tare da samar da abubuwan ci gaba a biranen da sallar ta fado a kansu kamar yadda aka fara gani tun a birnin Yamai da wasu birane yanzu kuma a bana ta fado Tahoua.