1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka A Jaridun Jamus

June 30, 2009

Halin da ake ciki a Kongo da Somaliya ma sun ɗauki hankalin jaridun na Jamus.

https://p.dw.com/p/Ie4t
Wasu ´yan makarantar Jamus dake aiki don taimakawa yaran makaranta a AfirkaHoto: DW

Da farko dai zamu fara ne da rahoton da jaridar Berliner Zeitung ta gabatar a game da wani abin ban sha'awa inda kimanin 'yan makaranta kimanin dubu 16 suka kama aiki na yini ɗaya don amfani da kuɗaɗen da zasu tara akan taimakon takwarorinsu a Afurka. Jaridar ta ce:

"'Yan makaranta kimanin dubu 16 a makarantun yankin Brandenburg suka kama aiki na yini ɗaya a maimakon halartar ajujuwa akan abin da suka kira: "Ranar gudummawarka ga Afurka". Manufarsu shi ne amfani da kuɗaɗen da suka tara don taimaka wa shirye-shiryen bunƙasa ilimi a Afurka."

Yaƙi ba filin daga: wannan shi ne kanun wani rahoton da jaridar Neues Deutschland ta gabatar dangane da yaƙin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa duk da wata yarjejeniya ta zaman lafiyar da aka cimma. Jaridar ta ƙara da cewar:

Bilder aus dem Kongo
Tsoffin ´yan tawaye da ´yan gudun hijirar KongoHoto: DW / Schlindwein

"A maimakon zaman lafiya sai ƙara durmuya ake yi a cikin ƙazamin faɗa a yankunan da dama na gabacin Kongo, abin da ya haɗa har da wasu sassa na arewacin Kivu. Mutane sai daɗa shida mawuyacin hali na ƙaƙa-nika-yi suke yi fiye da zamanin baya. Akwai ma masu zargin cewar ita kanta ainifin yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma ita ce uammal'aba'isin ƙazancewar halin da ake ciki, saboda ta bai wa ƙungiyar tawaye ta CNDP dake da hannu a cikinta damar kutsa kai wasu yankunan da a da can ba ta shiga cikinsu, domin kuwa a yanzu ta waye gari a matsayin wani ɓangare na sojan ƙasar."

A Somaliya ma ana ci gaba da fama da tashe-tashen hankula, amma duniya ta yi ko in kula da lamarin a cewar jaridar Süddeutsche Zeitung a cikin wani sharhin da ta rubuta, ta kuma ci gaba da cewar:

Somalia Soldat aus Äthopien in Somalia
Sojan Ethiopiya a SomaliyaHoto: AP

"Birnin Mogadishu sai ƙara nutsewa yake cikin kogin tashe-tashen hankula lamarin da kusan a kullu-yaumin ya kan ƙara sanyawa mutane su fid da ƙauna a game da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar Somaliya. Su kansu sojojin kiyaye zaman lafiyar da aka tsugunar ba su da ikon taɓuka kome don lafar da ƙurar wannan rikici. A haƙiƙa ma dai duniya gaba ɗayanta tayi watsi da lamarin wanda hakan ya sanya kowace ƙasa ke ɗari-ɗari da shawarar tura sojojinta aikin kiyaye zaman lafiya a Somaliyar."

Ta la'akari da wannan mawuyacin halin da ake ciki a ƙasar Somaliya ne jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung take bayyana mamakin ganin cewar shugaban riƙon ƙwarya Sharif Sheikh Ahmad, wanda hatta a birnin Mogadishu baya da wani ƙaƙƙarfan angizo ya kafa dokar ta-ɓace ta hana fitar dare. Amma kuma jaridar ta ce mai yiwuwa hakan ta taimaka shugaban dake samun goyan baya daga MƊD ya samu ci gaba bisa manufa.

Mawallafi: Ahmadu Tijani Lawal

Edita: Mohammad Nasiru Awal