1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taimakon yara mata inganta lumbu a Yuganda

March 1, 2017

A Yuganda manoni mai suna Eric Kaduru da matarsa Rebbeca da suke tafiyar da sana'ar itatuwa na kayan marmari, sun gano noma a matsayin wata hanyar karfafa yara mata wadanda suka bar makaranta kuma adadinsu ya yi yawa.

https://p.dw.com/p/2YS39
Weizenfeld
Hoto: AP

Bayan yin wasu bincike, Eric Kuduru ya gano cewar kusan babu harkokin noma a kasarsa, amma akwai wadatar kasa. Shekaru hudu a baya, ya tabbatar da cewa hakan zai iya zama hanyar kasuwanci mai riba mai tsoka kana da alfanu ga al´ummar yankunan karkara na Yuganda, saboda haka ya kirkiro da wani kamfani mai suna Kad Afirka da ke da burin tallafa wa 'ya'ya mata.

Yawanci manoman kasar Yuganda suna shuka tsirai ne don su ciyar da kansu da iyalensu, aikine da mata suka fi yin shi. Yanda babbar aiki kamar wannan ke tafiya, ba´a bukatan hanyoyi masu tsawo. Yan matan da Cibiyar kula da walwalar jama´a ta horar duk wadanda suka bar makaranta ne. Suna samun dama ta biyu wanda ba kasafai ba ake samu ba, don su yi dogaro da kansu kana suna biya wa kansu bukatu. A cikin su akwai Kengisa Ennete, Kafin ta shiga Kad Afrika tana samun dala uku ne duk wata, amma yanzu tana samun har dala hamsin.

Da zaran an horar, matan sukan samu sha´awar shuka yaya itatuwa, a Kasar da Kaduru ke basu haya a coci. A matsayin sa na dan kasuwa mai adalci, yakan sayi amfanin gona farashin kudin kasuw.

Bayan shekaru hudu, KadAfrika din ce da kanta ke samar da fiye da kashi 50 cikin 100 na kudaden shigar ta. Sauran aikin sha´anin kudi na samuwa ne daga cikin gida. Kimanin 'yan mata 1700 ne suka yi shirin a cewar Kaduru, amma ya ce  har yanzu dole ya shawo kan jam'a kan kyama da ake yi wa noma da ake gani a matsayin sana'a ce ta talaka.

Wannan shi ne babban kalubalen da mutanen ke fuskanta a kasar Yuganda. Yammacin Yuganda na da kimanin hekta miliyan 19 na kasar noma, sai dai kashi daya cikin 100 ne na kayan itatuwa da kayan lambu ake nomawa a yankin.