1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama a bangaren shari'ar Kamaru

Mohammed Awal Balarabe/ASMay 20, 2015

A ranar Larabar nan (20.05.2015) ake bikin cika shekaru 43 da hadewar Kamaru waje guda amma bikin ya zo lokacin da masu ruwa da tsaki a bangaren shari'a ke takaddama.

https://p.dw.com/p/1FTEa
Kamerun Präsident Paul Biya
Hoto: imago/Xinhua Afrika

Lawyoyin Kamaru da suka fito daga bangaren da ake amfani da turancin Ingilishi na so a mayar da hannun agogo baya, ma'ana a koma ga tsarin shari'a da kasar ke amfani da shi lokacin da take bin tsarin tarayya. A wancan lokaci dai yankin da ke amfani da Faransaci na dogara ne kan tsarin shari'a da ya gada daga Faransa da aka fi sani da suna "Droit Civil" wajen yanke hukunci. Yayin da jihohin kasar biyu da Birtaniya ta yaye ke bin "Common Law" a matsayin tsarin shari'a.

Sai dai kuma a yanzu, a kokarin mayar da kasar tsintsiya madaurinki daya, gwamnatin ta Kamaru ta na amfani ne da tsare-tsaren biyu a daukacin kasar, saboda haka ne ma a baya-bayannan ta nada alkalan da suka karanci tsarin dokoki irin na Faransa a yankin da ake amfani da turancin Ingilishi. Lawyoyin wannan yanki dai sun ce hakan bai dace ba, saboda tsaiko da ake fuskanta wajen yanke hukunci.

Kenia Wahl 2013
Lauyoyi a Kamaru na takaddama kan tsarin shari'ar da ya cancanta a yi amfani da shiHoto: DW/J. Shimanyula

Rabuwar kawuna tsakanin lauyoyin Kamaru

Su dai lawyoyin da suka nakalci tsarin shari'ar Birtaniya na "Common law" sun dibarwa gwamnati ta Kamaru wa'adin watanni shida domin ta gyara kura-kuranta. Idan ko fadar mulki ta Yaounde ta ki kallo wannan bukata tasu da idanun basira, to za su shiga yajin aikin da ba su san ranar janye shi ba.

Sai dai kuma lawyoyin da ke amfani da tsarin shari'a na Faransa ba sa goyon bayan takwarorinsu da ke amfani da tsarin shari'a na Ingila. Suna masu cewa an shafe shekaru ana tattaunawa kan tsarin shari'a na bai daya kafin a fara aiwatar da shi. Sannan kuma batun harshe ba zai taba zama wata madogara ba saboda bisa ga tsarin Kamaru kowa na da 'yanci amfani da yaren da ya ke so imma Faransanci ne ko kuma Ingilishi.

Hasashe na kokari na raba Kamaru gida biyu

Tuni dai wadanda suke nazarin harkokin yau da kullum a kamaru suka fara danganta bukatar lawyoyin da ke magana da ingilishi da wani yunkuri na sake dara kasar gida biyu. Da ma dai wasu 'ya'yan lardunan Arewa maso yammaci da kuma kudu maso yammacin Kamaru sun kafa wata kungiya tun shekarun da suka gabata da nufin raba gari da bangaren Faransaci. Sun zargin hukumomin Yaounde da mayar da larduna biyun da Birtaniya ta yi wa mulkin mallaka saniyar ware, alhali wannan yanki ne ya kunshi arzikin man fetur da ke samar wa kasar da kundin shiga.

NO FLASH Paul Biya Präsident Kamerun
Gwamnatin Shugaba Paul Biya ba ta kai ga tsoma baki kan wannan takaddama da ta kunno kai ba.Hoto: AP

Tun dai ranar 20 ga watan Mayu na shekarar 1972 ne sassa Kamaru da ke amfani da faransaci da kuma Ingilshi suka cimma yarjejeniyar yin watsi da tsarin tarayya tare da rungunar tsarin jamhuriyar, lamarin da ya sa Kamaru zama tsintsiya madaurinki daya.