1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama game da kafa gwamnatin hadin kan kasa a Nijar

August 2, 2013

Hakan ya biyo bayan rashin jituwa ne tsakanin shugaban kasar da ''yan adawa dangane da batun bangaran da ya kamata ya riki mukamin Firaminista a sabuwar gwamnatin.

https://p.dw.com/p/19J6T
epa03142091 President of Niger, Mahamadou Issoufou delivers a speech during the opening ceremony of the 6th World water forum at Parc Chanot in Marseille, southern France, 12 March 2012. More than 1,000 high-level stakeholders are gathered in Marseille to share solutions to worldwide water problems and commit themselves to their implementation. EPA/GUILLAUME HORCAJUELO +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Wanann lamari dai ya zo ne a daidai lokacin da ya rage 'yan awoyi kalilan shugaban kasar ta Nijar ya gabatar da jawabinsa ga 'yan kasa albarkacin zagayowar cikon shekaru 53 da samun 'yancin kan kasar inda zai yi bayani kan batun karkare wanann shiri nasa.

To sai dai bisa dukkan alamu assalatu na kan hanyar warwarewa koma ta warware inji Malam Sabo Seidu mataimakin shugaban jam'iyyar MDC YARDA mamba a kawancen jam'iyyun adawar na ARN biyo bayan wani taro da shugabannin jam'iyyun adawar suka shirya a ranar Juma'a a birnin Yamai domin nazarin sakamakon da wata ganawa da shugabannin 'yan adawar suka yi da shugaban kasa a ranar Alhamis kan batun.

Takaddama kan mukamin firaminista


A ranar Alhamis dai shugaban kasar Nijar ya yi wata ganawa ta musamman da
shugabannin 'yan adawar a fadarsa da nufin karkare zancan shigarsu cikin gwanmnatin hadin kan kasar da zai tabbatar a cikin jawabin da zai gabatar wa 'yan Nijar cikin jawabin nasa na ranar Juma'a to amma taron nasu ya watse baram-baram bayan da shugaban kasar ya sanar da su cewa zancan ba su mukamin firaminista bai taso ba, kamar dai yadda shugaban jam'iyyar PNDS TARAYYA na riko Malam Bazum Muhamed ya yi ma gidan rediyon DW karin bayani.


Sai dai ga bisa dukkan alamu akwai baraka a cikin jam'iyyar MNSD NASARA madugar 'yan adawa a kan wanann batu domin kuwa wasu daga cikin kusoshin wannan jam'iyya da ba su so in nadi muryarsu ba sun ce ya zuwa yanzu jam'iyyar tasu ba ta kai ga tsaida magana daya ba a kan batun a yayin da kuma wasu daga cikinsu suka ce labudda matsayin da kawancen 'yan adawar na ARN ya dauka shi ne matsayin jam'iyyar ta MNSD NASARA. Ko ma dai mai ake ciki a ranar Asabar ake yinta ta kare wai 'yan magana suka ce ramamme ya zagi maye inda kawancen jam'iyyun adawar na ARN zai fitar da sanarwa inda zai bayyana hakikanin matsayin nasa dangane da wanann batu na shiga gwamnatin hadin kan 'yan kasa biyo bayan jawabin da shugaban kasar.

Titel: Seini Oumarou, Vorsitzender der Partei MNSD im Niger Schlagworte: Niger, Oumarou, Opposition, MNSD Wer hat das Bild gemacht?: offizielles Bild (MNSD) Wann wurde das Bild gemacht?: 2013 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Niamey, Niger Bildbeschreibung: Bei welcher Gelegenheit / in welcher Situation wurde das Bild aufgenommen? Wer oder was ist auf dem Bild zu sehen? Seini Oumarou ist Vorsitzender der Partei MNSD-Nassara (Mouvement National de la Société de Développement ) und seit April 2011 Oppositionsführer im Niger. Zuvor hatte er in der Stichwahl um die Präsidentschaft gegen Mahamadou Issoufou verloren.
Seini Oumarou na jam'iyyar MNSDHoto: MNSD

Mawallafi: Gazali Abdu Tasawa
Edita: Mohammad Nasiru Awal