1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Batun bakin haure na neman janyotakun saka a kasashen EU

Lateefa Mustapha Ja'afarJune 15, 2015

Firaministan Italiya Matteo Renzi ya ce kasarsa za ta yi gaban kanta wajen magance matsalar bakin haure da ke biyowa ta tekun Bahar Rum domin shigowa Turai.

https://p.dw.com/p/1FhfE
Bakin haure a gabar teku da ke kan iyakar Italiya da Faransa
Bakin haure a gabar teku da ke kan iyakar Italiya da FaransaHoto: picture-alliance/dpa/C. Alessi

Renzi ya bayyana haka ne a yayin wani taron manema labarai da ya gudanar tare da shugaban kasar Mexico Enrique Pena Nieto. Renzi ya ce in har ba za ta samu taimakon kungiyar EU ba, to kasarsa za ta dau matakin da take ganin ya dace da ita yana mai nuna takaicinsa bisa yadda Faransa ta koro bakin hauren da suka isa kan iyakarta da Italiya domin neman mafaka, inda ya ce babu son kai ko kuma rufe idanu a kan matsalar bakin hauren. Renzi ya kara da cewa in har nahiyar Turai na son ci gaba da kasancewa Turai to tilas ne sai an hada kai domin shawo kan matsalar bakin hauren, in kuwa ba haka ba to tabbas Italiya za ta yi gaban kanta ba tare da bata lokaci ba wajen tunanin abin da kaje ya zo. Faransan dai a ta bakin ministan harkokin cikin gidan kasar Bernard Cazeneuve ta ce dole ne Italiya ta dauki nauyin bakin hauren da suke biyowa ta kasarta.