1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama tsakanin Turkiyya da Rasha ta yi zafi

Umaru AliyuNovember 24, 2015

Turkiyya ta ce jiragen saman yakinta sun harbo wani jirgin saman Rasha, bayan da Turkiyyar ta yi zargin cewar jirgin ya keta sararin samaniyarta.

https://p.dw.com/p/1HBza
Türkei Kampfjet f-16
Hoto: Reuters/M.Sezer

Rundunar sojan Turkiyya ta ce akalla sau goma ne take gargadin jiragen saman yakin wasu kasashe dabam da ke keta sararin samaniyarta ba tare da izini ba. Shi kansa jirgin yakin Rasha da aka harbo shi a ranar Talata, sai da aka yi masa gargadi sau da dama, amma ya ki bin umurnin kiran da aka yi masa ya janye daga samaniyar kasar Turkiya din. A daura da haka, ma'aikatar tsaron Rasha a Mosko ta musunta cewar jirgin yakin nata, samfurin SU-24, ya shiga sararin samaniyar Turkiyya, kuma ta ce yana shawaginsa ne a kusa da iyakar Turkiyya da Siriya a lokacin da aka harboshi. Sai dai wani dan jarida na Turkiyya da ke bayani game da wannan hadari ya nunar da cewar:

"Manufofin Rasha a wannan yanki babu shakka dabam suke da yadda Turkiyya take kallon al'amura a yankin. A bisa ra'ayin Turkiyya, ba tilas ba ne sai Turkiyya ta jira wani jirgin saman yaki ya keta sararin samaniyarta kafin ta harbo shi. Kasar tana iya daukar wannan mataki da zaran ta lura da cewar jirgin yakin yana kusantar iyakokinta, saboda Turkiyya din ta tsaida nisan da jirgin saman wata kasa zai kai kafin ta yanke shawararar yana kusantar iyakokin nata. Duk kuwa jirgin da ya wuce wannan wa'adi za a gargadeshi kafin a nemi harboshi."

Yayin da Pirayim ministan Turkiyya, Ahmet Davutoglu ya ce kasarsa tana da cikakken 'yancin daukar duk matakan da take ganin sun dace domin kare kanta, shi kuwa shugaban Rasha, Vladimir Putin ya yi Allah wadai da matakin da Turkiyya ta dauka na harbo jirgin saman yakin nata, inda ya ce hakan wani babban koma baya ne a yakin da kasashen duniya suke yi kan yan ta'adda na kungiyar IS a kasar Siriya.

Tsamin dantgantaka tsakanin Mosko da Ankara

Tun lokacin da Rasha ta fara kai hare-hare kan mayakan IS a kasar Siriya dangantaka ta fara tsami tsakaninta da Turkiya. Shugabanni a birnin Ankara ba ma suna dari-dari da matakan Rasha na keta iyakokin Turkiya ba ne, amma har suna baiyana rashin jin dadinsu a game da ayyukan jiragen saman yakin Rasha na jefa bama-bamai kan yan ta'adda na kungiyar IS. Ranar Litinin Pirayim minista Davutoglu ya kai karar Rasha gaban Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, saboda abin da ya kira, gallazawar da Rashan take yi wa Turkawa tsiraru mazauna Siriya sakamakon hare-haren nata. A korafin da ya yi, Davutoglu ya ce:

Türkei Premier Minister Ahmet Davutoglu
Pirayim ministan Turkiyya Ahmet DavutogluHoto: picture-alliance/dpa/S. Suna

"Bai kamata wata kasa guda ta yi gaban kanta a matakan yaki da 'yan tarzoma na kungiyar IS ba. Wannan abun da ya kamata ya zama na hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa. Bai kamata Rashan ta fake da kai hare-hare kan 'yan tawaye ko 'yan ta'addan Siriya amma tana jefa bama-bamai kan al'ummar Siriya da ba su ji ba, ba su gani ba, ko tsirarun Turkawa 'yan Turkmenistan da ke zaune a kasar ba".

Bayan hadarin a wannan Talata, ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov ya soke ziyarar da aka shirya zai kai Turkiyya, yayin da gwamnati a Mosko ta kira jakadan Turkiyya a Rasha domin baiyana masa matukar bacin ranta kan abin da ya faru. A daya hannun kuma, shugaban majalisar kungiyar Tarayyar Turai, Donald Tusk ya nemi duka wadanda ke da hannu a wannan sabani su kwantar da hankalinsu. Ya ce a wannan lokaci mai matukar hadari bayan harbo jirgin saman yakin na Rasha da Turkiyya ta yi ana bukatar nazari a tsanaki cikin kwanciyar hankali.