1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Ruwanda da Kwango sun dauki hankalin jaridun Jamus

Usman Shehu Usman M. Ahiwa
June 24, 2022

Rikicin kasar Kwango da taron kasashe rainon Ingila da ake yi a Ruwanda da mamayar da China ta yi wa kasuwanni da sauran harkoki a Afirka sun dauki hankali a wannan mako.

https://p.dw.com/p/4DCyH
Unruhen an der Grenze zwischen DRK und Ruanda
Hoto: Michel Lunanga/AFP/Getty Images

Za mu bude sharhunan ne da Frankfurter Allgemeine Zeitung, inda jaridar ta ce rikicin Kwango da Rwanda da ke karuwa. Gabashin Kwango ya sake zama wurin da ake gwabza fadan soji a kan iyakar kasar da Ruwanda. Kamar yadda kafafen yada labarai suka ruwaito, wata fitacciyar kungiyar ‘yan tawaye ta yi nasarar kwace garin Bunagana da ke kan iyaka a farkon makon jiya. Garin dai muhimmin wuri ne na kungiyoyin agaji da tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Kwango, MONUSCO. A karshen makon da ya gabata, Kwango ta rufe kan iyakarta da Ruwanda bayan da aka kwashi lokaci ana takun saka tsakanin kasashen biyu. ‘Yan sandan Ruwanda sun harbe wani sojan Kwango a kusa da kan iyaka.

Ruanda Kigali |  2022 Commonwealth Heads Of Government Meeting
Hoto: Luke Dray/Getty Images

Sai Jaridar die tageszeitung wacce ita ma ta yi labarin kasar ta Ruwanda amma jaridar ta hada rikicin da ya faru da kuma taron kolin shugabannin kasashe renon Ingila, inda ta ce kasar Ruwanda ita ce kasa ta farko da ba ta taba zama karkashin mulkin Birtaniya ba da ta karbi bakuncin taron koli na kungiyar Commonwealth. Sai dai matsalar tsaro da ke kara tabarbarewa a kan iyaka da makwabciyarta Kwango na haifar da cikas. A karkashin tsauraran matakan tsaro, an fara gudanar da bukukuwan da suka shafi taron kolin kasashen rainon Ingila wato Commonwealth a Kigali babban birnin kasar Ruwanda. Taron da aka sani da "CHOGM 2022" a takaice, ba kawai taron kolin Commonwealth na farko ba ne a Ruwanda, amma kuma na farko da ba zai gudana a kasar da ba tsohuwar mulkin mallaka na Birtaniya. Wannan ya kara bayyana musamman a taron lokacin da Firaminista Boris Johnson da Yarima Charles suka shiga zauren taron.

Ita ma jaridar Berliner Zeitung, ta yi sharhinta ne kan rikicin kasashen Turai da suka yi wa Afirka mulkin mallaka da kuma kasar China. Inda ta ce a wani bincike da aka gudanar, ya aza babbar  ayar tambayi a kan wadanda ke yanke shawara kan Afirka game da rawar da China da nahiyar Turai ke takawa a Afirka. Jaridar ta ce abubuwan da aka gano dai suna da ban tsoro. Turawan na cewa ko da yake sun yi hasarar kasuwanci bayan da kamfanonin kasar China suka karbe musu cinikayya da kasashen da Turai ta rena, amma dai a cewar masanan musamman daga kasashen na yamma, 'yan Afirka ba za su ji dadin kasuwanci da China ba a cikin dogon lokaci. Misali, turawa na daukar gadoji da manyan tituna da gine-ginen ofisocin da kasar China ke aiwatarwa a matsayin marasa inganci. Na biyu kuma, gwamnatocin Afirka da 'yan kasar nan ba da jimawa ba za su gane cewa Beijing ta lalata su; tarkon bashi yana rufewa. Ayyukan raya kasashen nan gaba da wuya a iya aiwatar da su. A wannan lokacin ne Afirka za ta sake juyawa daga Asiya tana neman kasashen yamma.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani