1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddamar siyasar jamhuriyar Bene

Abdourahamane Hassane MA
April 5, 2017

Majalisar dokokin kasar Bene ta yi watsi da bukatar karin wa'adi ga shugaban kasa ta hanyar kuri'a. Shugaban kasar ne ya bukaci hakan yayin da yake cika shekara guda kan madafun iko.

https://p.dw.com/p/2ajK7
Der Präsident von Benin Patrice Talon
Shugaba Patrice Talon a wani taro da ya halarta a Dakar, babban birnin kasar SenegalHoto: Getty Images/AFP/Seyllou

Wannan kuri'ar da 'yan majalisar Jamhuriyar Bene suka kada ta kin amincewa da yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin kasar wani abin ba zata ne da ya riski shugaba Patrice Talon wanda ya gabatar da kudurin da nufin takaita wa’adi daya kacal na shugaban a kan gadon mulki na tsawon shekaru shidda tare da 'yancin daidaito tsakanin maza da mata da kuma samar da kudaden tafiyar da harkokin ga jamiyyun siyasa, da dai wasu sauran dokoki. Ana bukatar samun kashi biyu bisa uku na kuri'ar 'yan majalisar kafin samun rinjaye, to sai dai galibin 'yan majalisun sun kada kuriar kin amincewa da dokar. Laurent Motegnon na daya daga cikin shugabannin kungiyoyin kwadago wadanda suka yi zaman durshen a gaban majalisar a lokacin da take tattauna kudirin cewa ya yi.

"Wannan kudiri na yin kwaskwarima ga kudin tsarin mulki, an jingine shugaba Talon ba shi da hurumi ko izini na yin sa, ya ce al'uma ce kadai ke da 'yancin bayyana matsayi tare da yanke shawara a kan wannan kudiri.''

Benin Präsidentschaftskandidat  Abdoulaye Bio Tchane
Abdoulaye Bio Tchane daya daga cikin jiga-jigan 'yan siyasa a BeneHoto: picture-alliance/AA

Tun da farko dai Shugaban na Benen yana da goyon baya sossai a majalisar dokokin kasar to amma ganin irin yadda aka kwashe kwanaki ana samun kai ruwa rana tsakanin gwamnatin da kungiyoyin kwadago da na daliban da ke adawa da kudirin, wannan ya sa 'yan majalisar suka ci tuwon fashi. Kuma wani abin da ya kara tayar da hankali shi ne cewar a makon da ya gabata ministar tsaro ta kasar Candid Armand Marie daya daga cikin na hannun damar shugaban ta ajiye mukaminta saboda halin da kasar ta shiga na bore saboda kudirin. Victor Topanou, wani masanin kundin tsarin mulkin Bene din ya ce dama ya san kur'iar ba za ta yi nasara ba.

"In da ma gyaran fuskar kudin tsarin mulki za a yi shi ne saboda wata matsala da ta kunno kai, idan da haka ne babu wanda zai kin amincewa, amma gyaran fuska ne ake son yin  gwaninta. Ya ce irin wannan kafin ka yi shi sai ka samu hadin kan jama'a baki daya, idan babu hadin kan, to za a gamu da wahala."

Wannan al'amari dai ya zo ne a daidai lokacin da shugaban na Bene Patrice Talon ke cika shekara guda a kan gadon mulki wanda tun a lokacin yakin neman zaben ya sha alwashin kawo sauye-sauye ga kundin tsarin mulkin kasar wanda aka amince da shi tun a shekara ta 1990 a lokacin da kasar ta kawo karshen mulkin soji.