1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddamar 'yan gudun hijra a duniya

Mohammad Nasiru Awal AH
June 22, 2018

Jaridar Süddeutsche Zeitung, wadda albarkacin ranar tunawa da ‘yan gudun hijira da ake yi a ranar 20 ga watan Yunin kowace shekara, ta mayar da hankali kan sansanin ‘yan gudun hijira na Dadaab da ke kasar Kenya.

https://p.dw.com/p/306OX
Kenia Das Flüchtlingslager Dadaab
Hoto: Getty Images/AFP/T. Karumba

Jaridar ta fara ne da cewa Dadaab ya kasance budadden kurkuku. Ta ce tun da dadewa sansanin ‘yan gudun hijirar da ke kusa da kan iyakar kasar Kenya da Somaliya ya kasance sansanin ‘yan gudun hijira mafi girma a duniya, da ke zama mafaka ga mutane rabin miliyan. Da yawa daga cikinsu sun tsere ne daga yakin basasan kasar Somaliya. A 1991 bayan kifar da gwamnatin Shugaba Siad Barre a Somaliya, hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bude sansanin a matsayin masalaha ta wucin gadi ga ‘yan gudun hijira dubu 90 daga Somaliya. Yanzu sansanin ya zama gida ga dubun dubatan matasa da ba sa hangen wata kyakkyawar makoma a rayuwa, kuma ba a san lokacin da halin rayuwarsu zai inganta ba ko ma lokacin da za su koma gida ba, domin har yanzu ana fama da tashe-tashen hankula a Somaliya.

Kenia Das Flüchtlingslager Dadaab
Hoto: imago/Xinhua

'Yan gudun hijira na fuskantar kalubale a cikin sansanonin da ke karbarsu ko'ina a duniya

Tanzaniya ta fara amfani ne da wata na'ura don maganin masu kauracewa biyan haraji musamman kananan kamfanoni inji jaridar Neue Zürcher Zeitung.

Jaridar ta ce a wani gidan cin abinci ana amfani da na'urar da girmanta bai wuce tafin hannu ba don shigar da yawan kudin da masu cin abinci a wurin ke biya a wani mataki na samun karin kudin haraji ga gwamnati. A Afirka ana fama da matsala wajen samun haraji daga kananan masu sana'a da ba su da rajista. Amma kwalliya ta fara mayar da kudin sabulu dangane da wannan tsarin da Tanzaniya ta fara amfanin shi da wasu shekaru kalilan da suka wuce.  Daga cikin kasashen Afirka kudu da Sahara da ke amfani da irin wannan tsari na karbar harajin kayayyakin masarufi akwai Kenya da Malawi da kuma Ghana.

Gasar cin kofin duniya na kallon kafa da ke wakana a Rasha Senegal ta taka rawar gani

Russland WM 2018 Polen gegen Senegal
Hoto: Reuters/C. Hartmann

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung a wannan makon ta mayar da hankali ne kan rashin tabuka wani abin kirki daga bangaren kasashen da ke wakiltar nahiyar Afirkan a gasar cin kofin kwallon kafa a kasar Rasha.

Jaridar ta ce kasar Senegal ta kasance abin alfahari ga nahiyar Afirka domin ita kadai ta yi nasara a wasan farko da ta yi a gasar ta cin kofin duniya, duk sauran wakilai hudu sun sha kaye a wasan farko, hasali ma bayan wasanni na biyu wasu sun fara shirye-shiryen yin sallama da gasar ta bana. Jaridar ta ce nasarar da Senegal ta samu kan kasar Poland da ci 2 da 1 ta sa nahiyar Afirka gaba daya cikin farin ciki, har ma da yin tuni da gasar 2002 inda a wasan farko da ta yi da Faransa wadda a lokacin ke rike da kofin duniya, Senegal din ta doke Faransa da ci daya mai ban haushi. Fata dai a nan shi ne Senegal za ta share wa nahiyar Afirka hawaye gasar ta Rasha.