1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takun saka bisa kasafin kudi a Najeriya

Usman ShehuJune 28, 2013

Sabanin majalisar dokoki da fadar gwamnati, ya hana aiwatar da kasafin kudin bana

https://p.dw.com/p/18y8q
Nigerian Finance Minister Ngozi Okonjo-Iweala speaks at a press conference of African finance ministers at the 2013 World Bank/IMF Spring meetings in Washington on April 20, 2013. AFP PHOTO/Nicholas KAMM (Photo credit should read NICHOLAS KAMM/AFP/Getty Images)
Ministar kudin Najeriya Ngozi Okonjo-IwealaHoto: NICHOLAS KAMM/AFP/Getty Images

A wani abun da ke zaman alamu na kama han'yar share watanni a cikin hali na rashin tabbas, al'ummar Tarayyar Najeriya sun share watanni suna jiran fara aiwatar da kasafin kudin kasar sakamkon rikicin da ke kara kamari a tsakanin majalisar wakilan Tarayya da ke da alhakin amince da kasafin kuɗi, wadanda kuma suka ce dole a yi gyara kan kasafin, yayinda ita kuwa gwamnati ta ce duk wani jinkiri zai sa al'ammura su tsaya cik a kasar.

A cikin makon da muke ciki ne dai 'yan majalisar suka sa kafa suka shure bukatar batun na kwaskwarima bisa kundin da ya share watanni shida ana kwallo da shi a tsakanin fadar gwamnatin kasar da zauren majalisun ta biyu. Abun kuma da ya tada hankalin fadar gwamnati da ta ce komai yana shirin ya tsaya a kasar, in har majalisar ba ta kai ga sake duba idon rahama kan kasafin ba. A wata wasikar da ya sake turawa gaban majlisar dai, shugaban kasar Goodluck Jonathan, yace misali asibitoci za su tsaya, haka gyara da sake ginin sababbin han'yo'yi, dama batu na wutar lantarkin da ya kasa kammaluwa a kasar.

Description en:House of Representatives of Nigeria Date 16 September 2005, 11:13 Source The House of Representatives Author Shiraz Chakera ou are free: to share – to copy, distribute and transmit the work to remix – to adapt the work Under the following conditions: attribution – You must attribute the work in the manner specified by the author or licensor (but not in any way that suggests that they endorse you or your use of the work). share alike – If you alter, transform, or build upon this work, you may distribute the resulting work only under the same or similar license to this one.
Majalisar dokokin NajeriyaHoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Abinda ke kawo tsaiko a tsakani

Babban matsalar dai na tsakanin fadar gwamnati da ta zargi majalisar dokokin da sauyin fasalin kasafin, tare da ragin kusan Naira milliyan dubu 72, a cikinsa da kuma majalisar da ta dage kan bisa nauyin kundin tsarin mulki da ya bata ikon gyara bisa ko wane sashen kasafin, domin amfanin al'ummar kasa. Dr Yarima Lawal Ngama dai na zaman karamin ministan kudin kasar ta Najeriya, kuma a fadar sa matakin majalisar babbar illa ce ga kokarin sauya rayuwar 'yan Najeriya.

Ikirarin yi wa jama'a aiki

Damuwa da ci gaban al'umma ko kuma kokari na son rai dai, daga dukkan alamu al'ummar kasar suna da jan aiki kafin iya gane makomar rikicin da ko wane bangare ke ikirarin yi domin su, amma kuma har yanzu suke jiran gani a kasa. Hon Yusuf Shitu Galambi dai, na zaman dan majalisar ta wakilai daga jihar Jigawa, daya kuma daga cikin jihohin da ministan ke zargin wakilansu da rashin kishin al'ummarsu, kuma a fadarsa ministan bai san nauyin al'umma ba.

LAGOS, NIGERIA - JULY 15: A detail of some Nigerian Naira,(NGN) being counted in an exchange office on July 15, 2008 in Lagos, Nigeria. (Photo by Dan Kitwood/Getty Images)
Wani dake kirga NairoriHoto: Getty Images

Ba bana kadai aka fiskanci wannan matsala ba.

Banbanci na fahimta ko kuma wayo na aci dai, an share shekara da shekaru ana aiwatar da kasa da kaso 60 cikin dari na kasafin kudi a duk shekara, sakamakon irin wadannan rigingimu da kan dabaibaye batun kasafin. To sai dai kuma an share shekarun tare da tasirin da ya kai ga kasar tara kudi masu yawa, amma kuma ba tare da tabbatar da sauyin da 'yan kasar ke fatan gani cikin kasar ba.

Mawallafi: Ubale Musa

Edita: Usman Shehu Usman