1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takun-saka tsakanin Ukraine da Rasha

March 15, 2014

Hukumomin Kiev na Ukraine sun gargadi Rasha da ta shiga taitayinta sakamakon ci gaba da jibge sojoji da kayan yaki da take yi a tsakanin yammaci da gabashin kasar.

https://p.dw.com/p/1BQMU
Ukraine Krim Flaggen Flagge Militär
Hoto: Reuters

Gwamnatin Ukraine ta zargi takwarta ta Rasha da mamaye wani bangare na kasarta ta hanyar jibge sojoji da jirage masu saukar angulu da kuma motocin sulke a wani gari da ke kusa da tsibirin Kirimiya. Wannan dai ba shi ne kutsen soji na farko da hukumomin Moscow suka yi a tsakanin yankunan yammaci da kuma gabashin Ukraine tun bayan fara takaddama tsakanin kasashen biyu ba. Sai dai kuma a wannan karon, cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin Kiev, ministan harkokin wajen Ukraine ya yi barazanar yin amfani da duk hanyoyin da suka wajaba domin ja wa sojojin Rasha birki idan Vladimir Putin bai janye dakarunsa ba.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ya rage sa'o'i a gudanar da zaben raba gardama a tsibirin Kirimiya inda za a ba wa 'yan yankin damar zaban inda suke so su kasance tsakanin Rasha da kuma Ukraine. Kasashen Turai sun danganta zaben a matsayin haramtacce. Sai dai kuma a zauren Majalisar Dinkin Duniya, kasar Rasha ta hau kan kujerar na ki a lokacin da mambobin Kwamitin Sulhu suke kada kuri'ar yin tir da zaben na Kirimiya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Mohammad Nasiru Awal