1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takun sakar mahukunta da makiyaya

May 31, 2017

An kama hanyar sabon rikici a tsakanin gwamnatin jihar Benue da kuma Fulani makiyaya, inda kungiyoyin Fulanin tarayyar Najeriya suka ce ba su amince da dokar hana kiwo da gwamnatin jihar ta sa hannu a kai ba.

https://p.dw.com/p/2duNS
Hana kiwon shanu akan tituna a jihar Benue da ke Najeriya
Hana kiwon shanu akan tituna a jihar Benue da ke NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/P. Desmazes

An dai dauki lokaci ana kai kawo an kuma kai ga asara ta rayuka da daman gaske sakamakon rigingimun manoma da makiyaya can a jihar Benue da ke tsakiyar Tarrayar Najeriya. To sai dai kuma daga dukkan alamu ana shirin bude fage a tsakanin fulanin da ke cikin jihar game da sabuwar dokar da gwamnatin jihar ta kafa wadda ta saka hannu a kanta a makon da ya gabata, dokar kuma da ta haramta kiwo ga fulanin a cikin filin Allah. Sabuwar do kar da ke zaman irinta ta farko a sashen arewacin kasar dai, ta tanadi dauri na shekara biyar ko kuma zabin tara na Naira miliyan daya ga duk wani makiyayin da aka samu yana kiwo a cikin filin Allah, Sannan kuma shannun da ba su da makiyayi to za a dora musu haraji mai nauyi kamin daga baya akai ga gwanjon su ga al'umma ta jihar a karkashin dokar da ke da fatan kai karshen rigingimun da suka mamaye sassa na jihar a can baya. To sai dai kuma daga dukkan alamu dokar ta harzuka masu sana'ar kiwon da kuma a fadar Abdullahi badejo da ke zaman shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ba za ta sabu ba wai bindiga cikin ruwa.

Makiyaya a Jamhuriyar Nijare sun koka game da yadda ake raba abincin dabbobi
Makiyaya a Jamhuriyar Nijare sun koka game da yadda ake raba abincin dabbobiHoto: AP

Kokarin take 'yancin Fulani

Kokari na take 'yanci na Fulani ko kuma kokari na kare matsala ta kisa dai, tun kafin Benue ita ma jihar  Ekiti a shekarar da ta shude tai nasarar kafa makamanciyar wannan doka a wani abun da ke zaman alamu na martani na jihohi ga gazawar mahukuntan tarrayar a cikin rikicin makiyaya da manoman. To sai dai kuma in har ta yi zafi ga Fulanin sabuwar dokar dai a fadar gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ta zama wajibi, akan hanyar kai karshen matsalar rashin tsaron da ke  jihar dama samar da dorarre na zaman a lafiya tsakanin kowa dama kare darajar manoma da makiyayan jihar. Daraja ta manoma ko makiyaya dai, daga dukkan alamu kotunan Tarrayar Najeriyar na zaman sabon fage na rikicin na manoma da Fulani da ya dauki tsawo na lokaci da kuma yanzu haka ke nuna alamun rikidewa a fadar Badejon da yace sun umarci lauyoyi da shigar da kara a gaban kotu da nufin tabbatar da hakkinsu cikin jihar mai tasiri. Abun jira a gani dai na zaman yanda take iya kayawa a gaban kuliya, tsakanin masu takama da sana'ar kiwon da kuma wasu a cikin jihohin kasar da ke musu kallon barazana ga rayuwar al'umma.