1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takunkumin EU ga Rasha na shafar kamfanonin Jamus.

August 7, 2014

Kamfanonin Jamus sun fara bayyana takunkumin da EU ta sanya wa Rasha da cewa babban kalubale ne ga harkokin kasuwancinsu.

https://p.dw.com/p/1Cr5o
Merkel Putin Symbolbild
Hoto: Getty Images

Kamfanoni a Jamus sun fara kokawa da irin takunkumin tattalin arziki da aka kakabawa kasar Rasha, babbar abokiyar kasuwanci ga mahukuntan na Berlin dama kasashen nahiyar turai. Kamfanonin da suke kula da harkokin tsaro da na kera motoci sun yi gargadin cewa kasuwancinsu na fiskantar barazana.

A shekarar bara Jamus ta kulla kasuwancin kayayyaki na Euro miliyan dubu 36 wato kimanin dalar Amirka miliyan dubu 48 kusan kashi daya bisa uku na irin kasuwancin da kasashen na EU suka kulla da kasar ta Rasha.

Sai dai duk da wannnan kiraye-kiraye na kamfanonin Shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Markel na ci gaba da bayyana goyon bayanta ga shirin na EU na goyon bayan takunkumin tattalin arziki ga wannan kasa.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Mohammad Nasiru Awal