1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin kawo karshen yaki a Afghanistan

Lateefa Mustapha Ja'afarJuly 15, 2015

Babban jagoran kungiyar Taliban Mullah Mohammed Omar ya bayyana goyon bayansa ga batun tattaunawa da gwamnatin kasar Afghanistan.

https://p.dw.com/p/1Fz9T
Jagoran kungiyar Taliban Mullah Mohammed Omar
Jagoran kungiyar Taliban Mullah Mohammed OmarHoto: picture alliance/CPA Media

Mullah Omar ya amince da tattaunawar tare da wakilan kasa da kasa domin kawo karshen rikicin kasar na tsahon shekaru 13 da ya tarwatsata. A yayin da yake jawabinsa na kammala azumin watan Ramadana Mullah Omar ya ce idan aka duba a addinance ma ba a haramta tattaunawar sulhu irin wannan dama musayar bayanan sulhu tsakanin makiya ba. Mullah Omar ya kuma bukaci mayakansa da su yi iya kokarinsu wajen ganin basa kashe fararen hula a yayin gudanar da ayyukansu ya na mai cewa kare hakki da rayuwar al'umma shine ayyukansu a addinance. A makon da ya gabata dai wakilan gwamnatin ta Afghanistan da kuma na kungiyar ta Taliban sun yi ganawar gaba-da-gaba a karon farko a kasar Pakistan domin warware yakin da suka kwashe tsahon shekaru suna gwabzawa a kasar.