1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taliban na ci gaba da karbe iko da biranen Afghanistan

Abdoulaye Mamane Amadou
August 13, 2021

Kungiyar Taliban ta karbe iko da birnin  Lashkar Gah a kudancin Afghanistan, bayan ta tsagaita wuta na tsawon sa'o'i 24 dan ba wa dakarun gwamnati damar ficewa daga yankin.

https://p.dw.com/p/3yw2s
Afghanistan Ghazni | Taliban Kämpfer
Hoto: Gulabuddin Amiri/AP Photo/picture alliance

Ko baya ga yankin  Lashkar Gah dai, a wannan Jumma'ar ma kungiyar ta Taliban ta sake karbe iko da Shagsharan babban birnin Ghor da ke tsakiyar kasar, kwana daya bayan da ta yi ikirarin kwace birnin Kandahar na biyu mafi girma a kasar.

A cikin tsukin kwanaki takwas din da suka gabata, Taliban ta karbe iko da kusan rabin manyan biranen Afghanistan daga hannun dakarun da ke biyayya ga gwamnati, a yunkurinta na dannawa zuwa birnin Kabul.

Wannan na zuwa ne a yayin da Amirka ta ambaci tura bataliyar soja dubu uku a birnin Kabul don kwashe ma'aikatanta, a yayin da Birtaniya ita kuwa ta ce za ta tura soja 600 don taimaka wa 'yan kasarta ficewa daga Afghanistan.