1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tallafawa mazauna gidajen yari a Najeriya

Ahmed Salisu
August 15, 2017

Wani matashi mai suna Isowo Smart ya dauki gabarar tallafawa mazauna gidan yari da wanda suka fito wajen koyar da su sana’oi gami da ceto wasu daga cikin su a Najeriya.

https://p.dw.com/p/2iHef
Symbolbild Gefängnis Afrika Gefangener
Hoto: Tony Karumba/AFP/Getty Images

Isowo Smart G. wanda matashi ne da ke zaune a Abuja babban birnin Najeriya a karkashin kungiyar da ya samar mai suna CPRI ta fara aikace-aikacenta ne kimanin shekaru bakwai da suka gabata abisa nuna alhinin yanayin da gidajen yarin Najeriya suka tsinci kan su kama daga cunkoso da rashin tsaftar bandakuna da rashin samun wadataciyar iska a dakuna kana uwa da uba rashin samun abinci a wadace a yayin da gidajen yari irin na Bauchi da Ningi da Misau an gina sune a tsakanin shekarun 1816 da1820 da 1827 ba sa samun wata cikakkiyar kulawa.

A hirarsa da DW, Isowu ya ce ''muna tallafawa wadanda ke zaune a gidajen yari da kuma wadanda suka fice daga gidan yarin a yayin da wadan da ke zaune a gidajen yarin muke musu abubuwa da yawa ta hanyar shirya musu bitoci don sake sajewa da jama'a da zarar sun fito domin in ba haka ba za su iya zama babbar barazana wajen kara fadawa aikata munanan laifuffuka, muna ganin muna rage yawan wadan da suke zaune a gidajen yarin ta hanyar tabbatar da ganin an samawa wadanda suke zaune haka ayyukan yi domin amfanar da alumma.''

Wannan yunkuri na Isowu dai ya sanya da dama daga cikin wanda suka amfana da wannan shiri  kyautata dabi'un wasu ma har sun tafi jami'oi. Baya ga wannan kuma, matashin da abokan aikinsa sun bawa wasu da kuma dabaru na kare kai daga aikata laifuka wanda zasu jefa su gidan yari. Tuni dai mutane da dama a Najeriya suka fara yin Allah sam barka da wannan tallafi da matashin ke badawa wanda suka ce zai taimaka wajen samar da al'umma mai cike da nagarta.