1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tallafi ga wanda tashin hankali ya shafa

Abdullahi Maidawa Kurgwi/ASMay 13, 2015

Jama'a na cigaba da bullo da kungiyoyi masu zaman kansu da nufin tallafawa wadanda tashe-tashen hankula na al'ummomi ke shafa a sassa daban-daban na tarayyar Najeriya.

https://p.dw.com/p/1FPFs
Nigeria Flüchtlinge wegen der Offensive gegen Boko Haram
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Daya daga cikin wadannan kungiyoyi dai ita ce kungiyar nan ta Lifeline Compassionate Global Iniciative wacce ke da hankoron tabbatar da zaman tare tsakanin Musulmi da Kirista a duniya. Makasudin kafa kungiyar shi ne janyo hankula al'ummar Najeriya game da muhimmancin zaman lafiya kamar yadda shugaban ta Pastor Markus Gamace ya sheda.

Nigeria Armee rettet Mädchen
Hoto: picture-alliance/dpa/EPA/Nigerian Army

Kasashen duniya irin su Amurka da Switzland da kuma tarayyar Jamus ne ke bada tallafi ga wannan kungiya, inda a zance nan da ake ma dai nan gaba cikin wannan wata na Mayu za ta bude wani sansanin 'yan gudun hijirar da kungiyar ta gina shi a Gurku da ke mararaban Habuja, inda za ta tsugunar da daruruwan 'yan gudun hijira Musulmi da Kirista a wani yunkuri na samun hadin kai da kaunar juna tsakanin mabiya addinan biyu.

Wannan kungiyar ta Lifeline Compassionate Global Iniciative, wacce ke da babban ofishi a TEKAN House da ke birnin Jos ta kan taimawa yara marayun da suka rasa iyaye mussaman ma wajen basu guraben karo karatu, kana mata da suka rasa mazaje ko dai ta hanyar tarzoma ko wani bala'i kan sami taimakon kungiyar kai tsaye.

Matasa da ke shiga faggen tashe-tashen hankula suma dai kungiyar ba ta barsu a baya ba domin kuwa ta kan sama musu sana'oi domin dogaro da kai kamar yadda Abdurahaman Aliyu Yaro shugaban matasa na wannan tafiya ya shaidawa wakilinmu Abdullahi Maidawa Kurgwi a wata hira da suka yi.

Nigeria Entführungen durch Boko Haram in Chibok
Hoto: DW/A. Kriesch

Yanzu babban aikin dake gaba shine samun tallafin hukumomi a Najeriya domin marawa tallafin kasashen duniya kamar su Jamus ta yadda za'a kyautata zaman tare tsakanin al'ummar kasa, mussamam ma wadanda tashe-tashen hankula kan shafa ko kuma suke zaman rashin yarda sakamakon banbancin addini ko kuma kabila.