1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tallafin Jamus ga Bangui

March 14, 2014

Kasar Jamus ta bi sahun kasar Faransa a yunkurin agazawa al'ummar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, domin samar da tsaro da abinci

https://p.dw.com/p/1BQ4l
Entwicklungsminister Gerd Müller in der Zentralafrikanischen Republik
Gerd Müller a BanguiHoto: picture-alliance/dpa

Tun bayan rincabewar al'amura a Jamuhuriyar Afirka ta Tsakiya, kasashen kungiyar Tarayyar Turai suka kuduri anniyar taimaka wa kasar, domin ta samu sake farfadowa, bayan da yanzu yaki ya wargaza kasar. A bisa irin wannan yunkurin ministan rayakashen Jamus Gerd Müller ya kai ziyara a Bangui babban birnin kasar domin duba halin da ake ciki.

A yanzu haka dai hukumomin Bangui suna neman taimako ta kowacce hanya, walau na jami'in tsaro da su tabbatar zaman lafiya, ko kuma agajin jinkai domin ceto kasar. Don haka ne ma tashar DW ta tambayi ministan raya kasashe na Tarayyar Jamus Gerd Müller, shin ko wane bangare kasar Jamus za ta iya taimaka wa al'ummar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, bisa halin tashin hankali da suke ciki, sai ya ce.

"Za mu yi aiki tare da hukumar ba da agajin abinci ta duniya, dakuma hukumar dake kula da samar da abinci mai gina jiki na duniya, domin mu tallafawa ayyukan da suke yi na samar da abinci a kasar. Babu yadda za a yi mu yi biris da halin da ake ciki. Al'umma dole ta kawo dauki bisa wannan mummunan halinda aka shiga a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, kuma muna da halin da za mu iya ba da taimako. Kama da bangaren inganta tsaro da samar da wadataccen abinci. Kama daga kiwon lafiya da samar da tsabtataccen ruwan sha, duk wannan za mu yi magana kan ayyuka da za mu aiwatar"

Zentralafrikanische Republik Unruhen 26.02.2014
Hoto: Reuters

Kusan dai su ma kansu kasashen Yamma sun fara yardar cewa, tuni ya kamata a ce sun agazawa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, amma kafin wannan lokacin kusan kasashen Yamma za a iya cewa sun yi watsi da ita bisa fannin raya kasa. Batun da shi ma kansa ministan raya kasashen Jamus ya tabbatar.

"Jamus ta amsa laifinta cewa, haka lamarin yake. Gabanin wannan lokacin bama gudanar da ayyukan raya kasa a nan. Amma a yanzu hakan zai sauya. A yanzu za mu bude ayyukan bada tallafi ba tare da bata lokaci ba. Kuma za mu fara tunanin ayyuka na gaggawa da kuma na tsawon lokaci"

To amma a cewa Martin Tumenta, jagoran dakarun kungiyar Tarayayar Afirka a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, ya ce a yanzu ba dogon surutu ake bugakata ba, amma tura dakarun da za su tabbatar da tsaro kawai ya kamata a yi.

Entwicklungsminister Gerd Müller in der Zentralafrikanischen Republik
Hoto: picture-alliance/dpa

"Bama iya tsaron daukacin kasar, idan mutum ya fadi haka ya yi karya. Wannan kasar a gaskiya tana bukatar sojoji su zo su taimaka, don inganta tsaron kasar"

An dai ruwaito ita kanta kasar Faransa da yanzu ke da dakaru kusan dubu biyu a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, tana mai cewa sojojin kiyayen zaman lafiya da Tarayyar Turai ta shirya aikawa, kawo yanzu ba su kai wani abu ba, domin haka ana matukar bukatar yin hubbasa cikin gaggawa. Yanzu haka dubban mutane ke ci gaba da barin kasar musamman Musulmai, inda wasu bakin da suka ganewa idanunsu suka bayyana cewa, har yanzu 'yan kungiyar mayakan Kiristoci ta Anti-Balaka na ci gaba da ayyukan ta'asa a wasu sanssan kasar. Domin kuwa babu jam'ian tsaron gwamnati, abin da kuma ya sa a yanzu kusan matasan kauyuka su ne ke kafa rundanar sa kai domin kare masu dibar ganima.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Pinado Abdu Waba