1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsarin rage wa jama'a radadin Corona a Jamus

Usman Shehu Usman GAT
June 4, 2020

Gwamnatin Jamus ta fitar da kudi kimanin Euro miliyan 50 domin tallafa wa kamfanonin da jama'a da nufin rage masu radadin matsalolin da annobar Coronavirus ta haifar masu.

https://p.dw.com/p/3dGGd
Deutschland Berlin Pressekonferenz zum Konjunkturpaket | Angela Merkel
Hoto: Getty Images/AFP/J. MacDougall

Gwamnatin ta Jamus ta cimma wannan matsaya ne bayan wata tattaunawa ta kwanaki biyu da jami'anta suka gudanar. Bayan musayar yawu da shugabannin suka yi dai, daga karshe sun fito tsarin mai matukar karfafa gwiwa fiye da tunanin mutane. Gwamnatin kasar ta Jamus ta kuma amince da rage haraji da kashi uku cikin dari har izuwa karshen bana. Olaf Scholz shi ne ministan kudi na kasar Jamus:


"Dole mu dau mataki a yanzu da Coronavirus ta haddasa katse harkoki baki daya. Dole mu tabbatar da cewa Jamus na da kudi a aljihunta da za ta iya ci gaba da zuba jari a kamfanoni, ta yadda haka zai tabbatar da 'yan kasuwa na samun masu sayan kayaki"


Tun makwanni ne dai shugabannin masana'antu a kasar ta Jamus ke yin kira don samun tallafin mai karfi daga gwamnatin kasar. Daga karshe dai yanzu ba wai kamfanonin ne kawai suka samu taimakon gwamnati ba, amma dukkan Jamusawa za su samu taimakon da aka yi kowa zai gani a aljihunsa. Wani abu da ke kara karfafa gwiwa shi ne yadda gwamnatin kasar ta Jamus ta ce, wannan Euro biliyan 50 somin tabi ne, akwai wasu hanyoyi da yanzu haka hukumomin ke dubawa don ceto kasar daga matsalolin da cutar Coronavirus ta kawo. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi karin haske:

Deutschland Baden-Württemberg | Coronavirus | Hotel Spielweg
Hoto: picture-alliance/dpa/P.v. Ditfurth


"Akwai karin wasu kwararan matakai da muke shirin fitarwa don mu kara tabbatar an farfado da tattalin arzikin kasar. Kuma nan gaba za mu amince da matakai da za a bi don cike gibin tattalin arziki don tallafa wa manya da kanan 'yan kasuwa"

Deutschland München | Coronavirus | Gastronomie
Hoto: Reuters/A. Gebert

Tattalin arzikin Jamus dai ya yi matukar samun illa sakamakon Coronavirus, amma kuma hukumomin Berlin sun sha alwashin ceto masanana'antun kasar. A cikin tsarin da suka yi ba wai 'yan kasuwa kawai ne za su ci gajiyarba, amma gwamantin ta sa dukkan 'yan kasar ciki, domin idan jama'a na da kudi to lokacin nan ne za sa su saye kayakin daga hannun 'yan kasuwa. Don haka ma'aikata za su samu ragi haraji kashi uku ciki dari, ga wadanda ke da iyalai kuwa, gwamnati za ta ba da Euro 300 ga duk da daya. Biranen kasar kuwa ko wannensu gwamnatin Tarayya za ta ba su kudi don rage asarar haraji da suka yi. Kamfanoni masu ba da horo su ma gwamnati ta yi akawarin tallafa musu. Manyan kamfanonin kera motoci su ma suna ciki, domin gwanmnati ta fidda tsarin na musamman ga motoci da ke amfani da lantarki. A gaba daya dai shugabar gwamnatin Jamus ta ce za a ware Euro biliyan 130 nan da badi. Wannan biliyoyin kari ne fa daga Euro sama da tiriliyan daya wanda tun a watan Maris gwamnatin Jamus ta amince da shi a matsayin kudin tsamo kasar daga matsalar tattalin arziki.