Tantanawa tsakanin Hamas da hukumomin Masar
October 31, 2006Talla
Wata tawagar ƙungiyar Hamas ta kai ziyara a Masar , da zumar tantanawa da hukumomin ƙasar a game da batun zaman lahia a yankin gabas ta tsakiya.
Tawagogin 2, za su masanyar ra´ ayoyi, a kan hanyoyin masanyar forsinonin yaƙi, tsakanin Palestinu da Isra´ila.
Hamas ta bayyana aniyar belin Gilad Shalit, sojan Isra´ila ɗaya, da ta yi garkuwa da shi, tun tun watan Juni da ya gabata, amma da sharaɗin Isra´ila, ta sallami mutane 1000, daga ɗimbin pirsinonin Palestinawa da ke cikin hannun ta.
Saidai tanatanwar na gunadana, a daidai lokacin da rundunar Isra´ila, ta kashe magoya bayan Hamas guda 2, da sanhin sahiyar yau , a Khan Yunes, dake zirin Gaza.