1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tantance masu zabe na yin nasara a Kano

Abdurrahman Kabir da Nasir Salis ZangoApril 11, 2015

Cikin irin nasarorin kuwa da ake samu sun hada da fitowar ma'aikatan zabe da wuri da ba su damar tantance duk wanda zai yi zaben kai tsaye.

https://p.dw.com/p/1F6HN
Nigeria Wahlen 2011 Bild 2
Hoto: DW/Gänsler

Rahotaani daga birnin Kano, birnin mafi yawan jama'a a arewacin Najeriya, sun bayyana cewa ana samun nasarar tantance masu zabe a wasu daga cikin mazabun birnin da wakilin DW Abdurrahman Kabir ya ziyarta. Nasarorin kuwa da ake samu sun hada da fitowar ma'aikatan zabe da wuri da ba su damar tantance duk wanda zai yi zaben kai tsaye ko da na'ura (card reader) ta gaza da kara wa'adin jefa Kuri'a har sai kowa ya gama.Don haka babu cunkoso kuma babu rigima kamar yadda aka samu a lokacin zaben shugaban kasa.

To sai dai a wasu sassan jihar ta Kano a cewar wakilin DW Nasir Salis Zango an sami karancin fitowar masu zabe a wurare da dama, amma tuni tantance masu zabe ta hanyar amfani da card reader ta yi nisa.