1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarayyar Turai da Birtaniya sun kasa cimma matsaya

Mohammad Nasiru Awal AH
July 20, 2017

Har yanzu babu wani ci gaba na a zo a gani da aka samu a tattaunawar ficewar Birtaniya daga kungiyar EU.

https://p.dw.com/p/2guDb
Brüssel Brexit-Verhandlungen, David Davis & Michel Barnier
David Davis na Birtaniya da Michel Barnier na Hukumar Tarayyar TuraiHoto: Reuters/Y. Herman

Bisa bayanan da babban mai tattaunawa na EU Michel Barnier ya yi, kungiyar tarayyar Turai da kasar Birtaniya suna nisa da cimma daidaito a zaman taron da suke yi game da ficewar Birtaniyar daga kungiyar ta EU da aka fi sani da Brexit. Barnier ya fada a birnin Brussels cewa akwai bambamcin ra'ayi babba kan 'yancin 'yan Birtaniya da 'yan kasashen EU da ke zaune a kasashen juna. To sai dai ministan Brexit na Birtaniya David Davis ya ce ya samu kwarin guiwa a tattaunawar. Bangarorin biyu dai sun bayyana haka ne bayan kammala zagayen farko na muhimman batutuwan da matakin ficewar Birtaniyar daga EU ya kunsa. A cikin watan Yuni bangarorin biyu suka fara tattaunawar.