1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarayyar Turai ta amince da yajejeniyar saka ido kan bankuna

December 13, 2012

Ministacon kudi na kasashe kungiyar Tarayyar Turai, sun amince da yarjejeniya hadin gwiwa ta saka ido akan harkokin bankuna

https://p.dw.com/p/171U1
Hoto: picture-alliance/dpa

Ministacon kudi na kasashe kungiyar Tarayyar Turai, sun amince da yarjejeniya hadin gwiwa ta saka ido akan harkokin bankuna cikin kasahsen, bayan shafe fiye da sa'o'i 14 ana tattaunawa a birnin Brussels na kasar Belgium.

Da sannan safiyar wannan Alhamis aka amince da wannan yarjejeniyar, kuma an shafe watanni ana jan kafa kafin kaiwa ga wannan matsayi. Tun da fari an amincewa da cewa babban bankin Turai zai saka ido kan harkokin bankunan kasashen.

Nan gaba ake gabatar da wannan daftari ga shugabannin kasashen, kuma cikin shekara ta 2014 yarjejeniyar za ta fara aiki cikin bankunan kasashe 27 da ke kungiyar ta Tarayyar Turai.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Halima Balaraba Abbas