1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarayyar Turai ta goyi bayan Macron

April 24, 2017

Hukumar tarayyar Turai ta bayyana goyon bayan ta ga dan takarar shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron a karawar da za a yi cikin kwanakin da ke tafe a tsakaninsa da Marine Le Pen.

https://p.dw.com/p/2boZP
Frankreich Präsidentschaftswahl EU Flagge
Hoto: picture alliance/Pacific Press/M. Debets

Tarayyar Turan dai ta ce goyon bayanta ga Macron da dalili, kasancewarsa mai ra'ayin kare kimar Turawa ne sama da wadda ta ce aniyar ta ba abar amincewa ba ce.

Dan takara mai zaman kansa Emmanuel Macron mai shekaru 39, ya yi nasara a zagayen farko, za kuma su kara da malama Le Pen a ranar 7 ga watan gobe na Mayu.

Macron dai tsohon ma'aikacin banki ne da kuma ya rike ministan tattalin arziki a gwamnati mai ci kafin daga bisani ya yi murabus ya kafa sabuwar jam'iyyarsa.

Idan har ya kaiga lashe zaben kasar, Mista Macron zai zama shugaba na farko ma fi karancin shekaru a tarihin kasar Faransa.