1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Diego Maradona

February 28, 2013

An haifi Diego Armendo Maradona ranar 30 ga watan Oktoba na shekara 1960 a garin Lanus na Arjentina.

https://p.dw.com/p/17oHx
FILE - In this June 29, 1986 file photo, Diego Maradona of Argentina, is lifted up as he holds the World Cup trophy after Argentina defeated West Germany 3-2 in the World Cup soccer final in the Atzeca Stadium, in Mexico City. (Ap Photo/Carlo Fumagalli, File)
Hoto: AP

Diego Armendo Maradona an haife shi ranar 30 ga watan Oktoba na shekara 1960 wato yanzu kenan ya na shekaru 52 da watani huɗu da aihuwa.An haife shi a wani gari mai suna Lanus dake ƙarƙashin mulkin babban birnin Buenos Airs.Ya na ɗaya daga cikin yara huɗu da iyayensa suka haifa.Tun ya na ɗan shekaru 11 a duniya a fara ɗaukar hankalin jama'ar ƙasar Arjentina game da irin hukumomin ƙwallo da ya laƙanta, saboda haka wani mai koyar da 'yan wasan Arjentina ya daukli shi a cikin ƙungiyar ƙwallon yara ƙanana ta ƙasar da ake kira Cebollitas.Maradona ya da shekaru 12 ya taɓa yin hira da wai gidan Talbajan inda ya ce shi burinsa a duniya shine idan ya girma ya halarci gasar cin kofin ƙwallo ta duniya tare da ƙungiyar ƙwallon Arjentina kuma ya ɗauko kofi, za mu zuwa gaba yadda Maradona ya cimma wannan buri.

A lokacin da ya cika shekaru 16 ya shiga ƙungiyar ƙwallon matasa ta ƙasa, inda ya zama jagoran 'yan wasan.Daga lokacin daga ya shiga wannan ƙungiyar har ya fita ba su taɓacin wani kofi ba na ƙasa da ƙasa, amma ya saka ƙwallaye raga har sau 115 a cikin wasanin 166 da ya buga.

Maradona ya fara samun galar farko a cikin ƙwallo a shekara 1979 a lokacin da aka yi gasar ƙwallan matasa ta duniya inda aka zaɓe shi ɗan wasan da ya fi taka leda a wannan shekara.

Ya buga wasa a manyan ƙungiyoyin ƙwallo daban-daban kamar Barça ta Spain kokuma SSC Naples, a ƙasar Italiya inda ya taimakawa fiye da kima wajen nasarori daban-daban da wannan ƙungiyoyin ƙwallo su ka samu.

Diego MARADONA, Argentinien, erzielt das legendaere Handtor ("die Hand Gottes") in der Begegnung England - Argentinien 1:2 bei der Fussball-Weltmeisterschaft 1986 in Mexico, 23.02.1986.
Diego Maradona 1986 ya saka kwallo raga da hannuHoto: picture-alliance / Sven Simon

Rawar da Maradona ya taka domin haskaka kwallon Arjentina da kuma na ƙungiyin ƙwallon ƙetare da ya buga wasa a ciki,kamar Barcelona da Nalpes:

Babu shakka Maradona ya taka mahimmiyar rawa, kuma za a gane hakan, ta hanyar kofifikan da ya kashe da kuma gallolin girmna da ya samu a lokacin da ya na buga wasa.Misali tare da shi Arjentina ta ci gasar kofin ƙwallon ta duniya har so biyu, wato a shekara 1986 da kuma 1990.

A Barça ya taimaka wajen ɗaukar kofi har sau biyu, a Naples dalili da ƙwazon da ya nuna, ƙungiyar ta ci kofinan wasanin Italiya har so biyar.

Hukumar ƙwallon kafa ta duniya wato FIFA ta shirya wane zaɓe ta hanyar Internet, inda ta buƙaci ma'abuta ƙwallo suka baiyana ra'ayin su game da ɗan wasan da ya fi shara a cikin ƙarni na 20.

Bayan an tattara ƙuri'un, Maradona ya lashe wannan zaɓe tare da kashi 36,27 cikin ɗari na mutane da su ka baiyana ra'ayoyi, sannan Pele ya zo na biyu tare da kashi 36,20 cikin ɗari.

Sannan a lokacin gasar cin kofin ƙwallo ta duniya a shekara 1986 shine a ka zaɓa a matsayin ɗan wasan da ya fi shahara.

A shekaru huɗu ƙungiyar 'yan jaridar da ke kula da wasanin motsa jiki ayankin Latine Amurika tana ayyanar da Maradona a matsayin ɗan wasan da ya fi ƙurewa wato a shekarun 1979,1980,1981 da kuma 1986.Ha ka dai yayi ta samun irin-iren wannan lamboyin yabo masu yawa wanda ba za mu iya zanawa ba gaba ɗaya.

Argentina head coach Diego Maradona gestures during the World Cup quarterfinal soccer match between Argentina and Germany at the Green Point stadium in Cape Town, South Africa, Saturday, July 3, 2010. (AP Photo/Martin Meissner)
Hoto: AP

Masu adawa da Maradona na zargin shi da wasu mummunan ɗabi'o'i da halayen da ba su dace ba:

Da dama daga ma'abuta ƙwallo su na zargin Maradona da rashin ladabi da kuma ɗaukar kai, sannan ga shi da fitina da kuma shaye-shaye,faɗace-faɗace shi ne ma ya kawo ƙarshen wasan da a Barça a shekara 1984 bayan ya haddasa wani rikici tsakanin magoyan bayan Barca da na Athletic Bilbao a lokacin buga gasar Sarkin Spain kuma gaban mai martaba sarki Juan Carlos.Daga ya koma SSC ta Naples a Italiya inda nan ma dai bai fasa tashin hankalin ba.

A jimilce tarmamuwar Maradona ta fara dushewa a shekara 1991 bayan da jami'an tsaro suka cafke shi tare da zarginsa da shan ƙwayoyi, kan ganja wiwi, hodar Ibilis babu irin ƙwayar da ya bari.

Dalili da haka aka dakatar da shi wurin buga wasa har tsawan watani 15.Bayan ya kammala hukunci sai kuma ya fita daga ƙungiyar Naples ya koma FC Sevilles kamin daga bisani gaba ɗaya ma ya tare zuwa ƙasar sa ta Arjentina, inda acen ma sannu a hankali tarmamuwar ta sa ta ci gaba da dushewa, kuma ƙurrewar ta sa ma ta fara ragewa.

To amma duk da haka, Arjentina ta saka shi daga jerin 'yan wasan da su ka buga wasa a gasar cin kofin ƙwallon duniya ta 1994 a ƙasar Amurika.Saidai wasa biyu kadai ya buga a wannan gasa domin bayan binciken da aka yi masa an gano bai daina shan miyagun ƙwayoyi ba a gasar cin kofin ƙwallon duniya ta Amurika Maradona ya yi wasan sa na karshe a ƙarƙashin ƙungiyar ƙwallon Arjentina kuma a nan ne ya saka ƙwallo mafi mamaki a cikin raga a yayin da Arjentina ke buga wasa da Girka.Baki ɗaya Maradona ya yi ritaya da buga ƙwallo a shekara 1997.

Sannan ya shiga wata babar matsala tare da jami'an karbar haraji na ƙasar Italiya wanda suka zarge da rashin biyan harajin da ta kamata ya biya lokacin da yayi zaman zama klasar, saboda haka su ka caje shi tarar euro miliyan 37.

o1.jpgArgentinean national soccer team head coach, Diego Armando Maradona, is seen during a training session in Buenos Aires, Argentina, on 22 May 2010. Argentina will take part on the Group B of the FIFA World Cup South Africa 2010 along Nigeria, South Africa and Greece. EPA/Cezaro De Luca +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture alliance / dpa

Sana'ar Maraona bayan yayi ritaya ta buga ƙwallo:

Bayan ya daina wasa Maradona sai ya rikiɗa zuwa ɗan jarida mai bada labarai game harkokin ƙwallo.Duk lokacin da ake buga wasa 'yan jarida masu bayar da rahotani game da wasan suna gaiyyato sa ya na yin sharhi game da wasan.

Banda wannan aiki an naɗa Maradona a matsayin mai koyar da 'yan wasan ƙwallon Arjentina a shekara 2008.A wasan farko 'yan wasan sun kara da na Scottland inda suka yi nasar ɗaya da nema.Shine ne ya kai 'yan wasan Arjentina a gasar cin kofin ƙwallo ta duniya a Afirka ta Kudu a shekara 2010, inda Jamus ta taka masu birki tare da ci huɗu da nema a wasan mai ma na kusa da na ƙarshe.

Bayan an koma gida a watan Juli na shekara 2010 hukumar ƙwallon Arjentina ta tsige daga matsayin mai koyar da 'yan wasan ƙasar.

Kusan shekara guda bayan ya sauka daga wannan muƙami sai Dubai ta ɗauke shi a matsayin mai koyar da 'yan wasan Club ɗin Al-Wasl Dubai.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Zainab Mohammad Abubakar