1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Hausawa

April 22, 2010

Tarihin Hausa bakwai da banza bakwai

https://p.dw.com/p/N3Yb
Noma da kiwo a ƙasar HausaHoto: AP

A ƙarni na 13 ne dai ƙasar Hausa tayi tashe harma take gasa da Daular Kanem-Borno da Mali. Haka kuma ƙasar Hausa ta yi fice wajen cinikin Zinari da Goro da Gishiri da fatu da ƙiraƙi da kuma leda. Daga shekarar 1804 zuwa 1808 kuma Shehu Usmanu Ɗan fodio ta yarda suka kasance a ƙarƙashin Dular Shehu Usmanu Ɗan fodio.

Garuruwan Hausa bakwai da Banza bakwai sun samo asali ne daga Auren Sarauniya Daurama ta Daura da kuma Umarun Baghadaza wanda aka fi sani da Bayajidda wanda tarihi irin na kunne ya girmi kaka ya nuna cewar wani Jarumi ne daya fito daga ƙasar Baghadaza. Da farko dai an ce Bayajidda ya fara yada zango ne a ƙasar Borno inda yake taimakawa Shehun wajen yaƙi kuma har takai ya auri ɗiyar shehun Borno na wancan lokaci. Koda yake ya bar Borno bayan da aka zargeshi da nema ƙwace sarautar Borno kafin daga bisani ya taho ƙasar Daura.

Koda yake kuma kafin ya zo Dauran ya fara yada zango a Garun Gabas da ke ƙasar Hadeja inda aka ce ita wannan mata daya taho da ita ta haifa masa ɗa guda. Daya isa Daura ya tarad da wata macijiya da ke hana ɗiban ruwa a wata rijiya mai suna rijiyar Kusugu, in banda ranar Juma'a.

An dai ce Bayajidda ya kashe wannan macijiya dalilin daya sa kuma Sarauniya ta aure shi. Saboda haka Hausa bakwai da Banza Bakwai sune jikokin Sarauniya da kuma Saɗakan, wato Bawo wanda  Sarauniya ta haifa shine da 'ya'yansa shida suka kafa hausa bakwai. kuma ɗan da Saɗakar Sarki ta haifar masa shine ya kafa Hausa banza bakwai.

Ƙasashen Hausa bakwan dai sun haɗa da Daura  da Kano da Katsina da Zazzau   da Gobir da Rano da kuma Biram ko kuma Haɗeja.

A yayinda kuma Banza bakwai suka haɗa da Zamfara da Kebbi da Yauri da Gwari da Kwararrafa ko Jukun da Nupe da Kuma Ilorin. To sai dai wannan kamar yadda Farfesa Ibrahim Malumfashi na tsangayar tarihin Hausa a Jami'ar Usmanu Ɗan fodio shine cewar, akasarin wannan tarihi ne da masana ke ɗaukansa na kunne ya girmi kaka.

Mawallafi: Babangida Jibril Edita: Zainab Mohammad