1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Kofi Anan

Abba BashirDecember 5, 2005

Takaitaccen tarihin Kofi Anan

https://p.dw.com/p/BvVi
kofi Anan
kofi AnanHoto: dpa

Masu sauraron mu assalamu alaikum barkan mu da sake saduwa cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin dake amsa tambayoyin masu sauraro.

Tambaya-Fatawar mu ta wannan makon ta fito ne daga hanun mai sauraron mu a yau da kulum Saidu Gangara fada Radiyo makaranta BP 144 Maradi a jamhuriyar Niger,mai sauraron namu cewa bayan gaisuwa da fatan alheri,don Allah ku bani tarihin sakatare janar na majalisar dikin duniya Kofi Anan.

Amsa-An haifi Kofi Anann ne a birnin Kumasi na kasar Ghana a ranar 8 ga watan Afrilun shekara ta 1938,ya kuma yi karatunsa na jami’a a jami’ar kimiya da fusaha ta Kumasi,kuma ya kammala bincike na degreensa a fanin ilimin tattalin arzikinkasa a jami’ar kwalejen Macalester dake birnin St.Paul Miniestota a kasar Amurka a shekata ta 1961.

Daga 1961 zuwa 1962,Kofi Anan yayi karatu a fannin ilimin tattalin arzikin kasa a sashen nazarin ilimin tattalin arziki na jami’ar des Hautes Etudes Internatinale ta Geneva.A shekara ta 1971 zuwa 1972 Kofi Anan ya zamanto mutumin da yayi karatu a kwalejen kimiya da fasaha ta Massachusetts A Amurka,anan din kuma ya sami baban degree a fanin kimiyar tafiyar da ragamar mulki.

Mr.Anan ya fara aiki da majalisar dinkin duniya ne a matsayin jami‘i mai lura harkokin gudanarwa da kasafin kudi,a bangaren hukumar lafiya ta majalisar dikin duniya dake da mazaunin ta a birnin Geneva.Tun daga wanan lokacin dai Kofi Anan yayi aiki a karkashen hukumar dake lura da bunkasa tsarin tattalin arzikin kasahen Africa dake da mazauni a birnin Adis Ababa na kasar Habasha.

Kofi Anan ya riki mukamin mukaddashin sakatare janar na hukumar tsaro da kare hakin bil adama ta majalisar dikin duniya a tsakanin 1987 zuwa 1990.

Mr.Kofi Anan dai ya riki mukamai da dama a majalisar dikin duniya,kuma shine ke zaman mutum na bakwai a jerin mutanen da aka zaba kann mukamin baban sakatare janar na majalisar dikin duniya.Ya dai fara rike mukamin baban sakatare janar na majalisar dikin duniya karo na farko a ranar daya ga watan Janairun 1997,bisa amincewar kwamitin sulhu da kuma baban zauren mashawartar ta majalisar dikin duniya.An kuma sake zabar Kofi Anan karo na biyu kan mukamin na sakatare janar na majalisar dikin duniya a ranar daya ga watan janairun shekara ta 2002,inda zai kare wa’adin aikinsa a ranar 31 ga watan Decemban shekara ta 2006 mai zuwa.Kafin dai a nada Kofi Anan kan mukamin baban sakatare janar na majalisar dikin duniya,Anan sai da Anan ya riki mukamin mukadashin sakatare janar din majalisar dinkin duniya mai lura da harkokin aiyuka na kiyaye zaman lafiya a kasahen duniya.A lokacin da aka cimma yarjejeniyar kawo karshen yakin Bosnia Hergovina,Mr Anana ya riki mukamin wakilin musanman na baban sakatare janar din majalisar dikin duniya zuwa tsohuwar Yugoslavia,inda aka dora masa a lhakin da harkokin mika mulki ga farar hula a Bosnia Herzgovina,domin a wanan lokacin sojin kiyaye zaman lafiya na majalisar dikin duniya,karkashin shugabancin kungiyar tsaron tekun Atlantica ta Nato aka dorawa alhakin gudanar da aiyuka na kiyaye zaman lafiya a Bosnia.Mr.Kofi Anan yayi amfani da mukaminsa na karamin sakatare janar mai lura da aiyuka na kiyaye zaman lafiya a kasahen duniya,wajen tabatar da zaman lafiya lokacin da aka fuskanci matsalolin tashe-tashen hankula ko siyasa a kasashe da dama na duniya,kamar dai shirin mika mulki ga hanun farar hula a Nigeria,rikicin bom din yankin Lokerbia tsakanin Amurka da Libya,sai kuma yunkurin na tabatar da zaman lafiya a gabashin Temo,tare kuma kokarin ganin an sami sulhu tsakanin Isra’ila da Palasdinawa karkashin kudirorin kwamitin sulhu na majalisar dikin duniya.A watan Afrilun shekara ta 2000,baban sakataren na majalisar dikin duniya Kofi Anan,ya gabatar da wani rahoto,inda ya bukaci kasahen duniya da su taimaka wajen gabatar da wani tsari da zai taimaka wajen yaki da talauci,tare kuma inganta manufofi na wayar da kan jama’a game da yaki da cutar kanjamau mai karya garkuwar jiki dake damun matalautan kasahe masu tasowa na duniya.Mr. Anan bai tsaya a nan ba,sai da kasashe masu arzikin masana’antu da su taimaka wajen kawo karashen matsaloli na yake yake da tashe tashen hankula da ake fama da su a kasashe da dama na duniya.A ranar 10 ga watan Disamban shekara ta 2001,aka baiwa Kofi Anan lambar gimamawar zaman lafiya ta kasahen duniya,bisa irin rawar da ya taka wajen tabatar da zaman lafiya a kasashe da dama na duniya.Baban sakataren dai na majalisar dikin duniya mutum ne da ya kware wajen yin magana da harshen turanci,Faransanci da kuma wasu harsuna na Africa.Ya na kuma auren wata mashahuriyar lauya ’yar kasar Sweden,kuma ta rubata littattafai da dama game da kananan yara da kuma majalisar ta dinkin duniya.Yanzu haka dai Mr.da kuma Mrs.Anan nada 'ya'ya uku.

Muna fata mai sauraron namu ya gamsu daa wanan amsa.