1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Mamman Shata

Abba BashirJuly 24, 2006

Bayani akan Marigayi Alh. Dr.Mamman Shata

https://p.dw.com/p/BvVM
Gangunan kida
Gangunan kida

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya:Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Malam Dan’azumi Saminu Zakari daga Jihar Lagos a Tarayyar Najeriya, Malamin ya ce don Allah ina so ku sanar da ni tarihin Marigayi Alhaji Dr. Mamman Shata Katsina, shin a ina ya soma waka, kuma wacce ce ta fi suna daga cikin wakokinsa?

Amsa: An dai haifi Marigayi Alhaji Dr. Mamman shata a garin Musawa, kuma ya girma a katsina wato Jihar Katsinan Tarayyar Najeriya. To a lokacin da Marigayi Dr. Mamman Shata ya ke a raye akwai tambayoyi makamanta wadanda Malam Dan’zumi ya tambaya, wadanda shi da kansa Shatan ya amsa su a rayuwarsa. Sabodahaka mun yi kokarin tsinto irin wadannan hirarraki da aka yi da marigayin lokacin da ya ke raye a Duniya.

An tambayi Marigayi Dr. Mamman Shata cewar a ina ya soma waka sai ya kada baki ya ce“A nan Musawa inda aka haife ni a nan na soma waka kuma duk inda na je yawo to da wakata suka ganni„

Ko wane dalili ya sa Dr. Mamman Shata ya soma waka a rayuwarsa, ga dai amsar da ya bayar“Dalili shine kiriniya ta yarinta kurum,bawai don gadon uwa ko uba ba, domin kuwa na dade ina yi bana kabar ko anini , in ma an samu kudi sai dai makada da maroka su dauka. Sai daga baya bayan na mai da waka sana’a na fara amsar kudi „

Shin waya sawa Dr. Mamman Shata wannan suna nasa wato Shata

Wanda ya sa mini wannan suna Shata sunansa Magaji Salamu, shine ya samin suna Shata Mijin mai daki, ita mai dakin kaka ta ce, ita ce ta haifi wanda ya haife ni„

Da aka tambayi Dr. cewar wace waka ce ta fi suna kuma ya fi jin dadin ta ko kuma ta fi birge shi a duk ilahirin wakokin da ya yi, sai ya ba da amsa kamar haka“ To wannan wani abune mawuya ci a wurina kuma kowa yace zai iya ganewa karya yake yi tunda shi shatan bai ganeba „

Bisa al’ada ga yanda mawakan Hausa suke yin wakokin su, akwai waka da suke yi wa kansu da kansu kirari a cikinta wadda aka fi sani da suna Bakandamiya. To shima Marigayi Dr. Mamman Shata bai yi kasa a guiwa ba wajen yi wa kansa irin wannan waka.

Daya daga cikin hikimomin da Allah ya baiwa Marigayin shine cewar yana iya kirkirar waka a duk lokacin da yaga dama ko kuma aka bukaci da ya yi hakan. Misali wakar da ya yi ta Dajin-runhu da kuma wakar da ya yi ta Canada Centre a lokacin da ya kai ziyara kasar Amurka.

Bisa al’adar Hausa, Mawaka sukan yi wa Mutane Waka, to amma a wani lokaci akan yi wa wakar mummunar fahimta, misali wakar da ya yi ta kusoshin Birni Uwawu da kuma wakar nan ta Na-malumfashi Habu Dan-mama, wanda masu fashin bakin wakoki su ke ganin cewa, wadannan wakoki ya yi sune domin ya nunawa Mutane cewar Yan zamanisun rasa inda za su kama, su basu kama Duniya ba kuma basu kama Lahira ba.To da aka tambayi Dr. cewar shin ko wannan bayani na masu fashin bakin wakoki haka yake sai ya ce“To wannan zance ne irin nasu , shi wanda naiwa ya san abinda na ce, kuma masu ji da basira sun san abinda na ce „

Daga cikin dalilan da suka sa Marigayi Dr. Mamman Shata ya ke yiwa Mutane Waka, a kwai kwarewa akan sana’a misali wakar da ya yi ta Bawa Direba. An tambayi Marigayi Mamman Shata, shin waye Bawa direba dinnan,kuma mai ya sa ya yi masa waka, kuma da gaske ne dukkanin abubuwan da ya fada a cikin wannan waka ta Bawa Direba, gaskiya ne haka abin yake, sai ya ce“Bawa jankin, shi kam Mutumin Katsina ne, amma a Musawa yai wayo, duk abinda na fadi a wakar Bawa haka yake ban kara masa ba, ban rage masa ba, kuma ko da ni ban fadi ba wani sai ya fadi „

Har ila yau Marigayi Dr. Mamman Shata yakan yi wa manyan shugabanni waka, mu samman ma wadanda suka tsayar da adalci, yanci, daidaito da kuma hadin kan al’umma, Misali wakar da ya yiwa Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, Allah ya ji kansa.

Sakamakon wakokin da marigayi Dr. Mamman Shata ya yi domin amfanin Al’umma, ya samu yabo da lambobin girmamawa. Misali a lokacin Mulkin Janar Gowon an ba shi lambar girma shi da marigayi Garba A.B.C.D. Kuma har ila yau Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta bashi Digirin girmamawa na Dr. wanda sakamakon haka ya sa ake kiransa Dr. Mamman Shata Katsina.